Majaisa Ga Tinubu: Ka Yaye Takunkumin Daukar Ma'aikata a Najeriya
- Majalisa ta bukaci shugaba Tinubu ya cire takunkumin ɗaukar ma'aikata aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya
- A cewar majalisar, shekaru da dama da suka shuɗe tsohon shugaban ƙasa ya kakaba takunkumin sakamakon matsin tattalin arzikin da aka shiga
- Sai dai ta ce duba da halin da yan ƙasa ke ciki bayan cire tallafin fetur, ɗaukar matasa aiki zai sauƙaƙa wa talakawa
FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaye takunkumin ɗaukar ma'aikata a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.
Rahoton The Nation ya tattaro cewa majalisar ta buƙaci shugaban ya cire takunkumin ne domin bada damar ɗaukar matasan 'yan Najeriya su cike guraben da ke akwai.
Hakan ya biyo bayan muhawara da amince wa da kudirin da ɗan majalisar tarayya, Honorabul Francis Ejiroghene Waive, ya gabatar a zaman yau Laraba, 19 ga watan Yuli.
Majalisar ta kuma roki hukumar kula da ma'aikatan Najeriya da sauran hukumomin da abun ya shafa su hanzarta biyayya ga umarnin shugaban ƙasa kan wannan batu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnati ta kakaba takunkumin ɗaukar aiki a baya?
Honorabul Waive ya tuna lokacin da tsohuwar gwamnatin Buhari ta sanya takunkumin ɗaukar ma'aikata a ma'aikatu da hukumomin gwamnati sakamakon karyewar ɗanyen mai da faɗuwar tattalin arziki.
Haka zalika ya ƙara tuna lokacin da majalisar tarayya ta 9, wacce ta gabata ta cimma matsaya kuma ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa ya cire takunkumin da ya ƙaƙaba.
Shin gwamnatin Buhari ta cire takunkumin a wancan lokacin?
A cewar ɗan majalisar, rahoton kafafen sada zumunta ya nuna cewa an cire takunkumin a wancan lokacin amma ba bu wata shaida ta ɗaukar ma'aikata a ko ina, Leadership ta ruwaito.
Ya ce tsawon shekaru ba a ɗauki sabbin ma'aikata ba, wanda hakan ya haddasa ƙarancin ma'aikata musamman a ɓangaren hukumomin tsaro, inda aka kara wa wasu girma, wasu kuma suka rasu.
Bugu da ƙari, ya ce cire takunkumin ɗaukar aiki da kuma ɗaukar matasa aiki zai zama wani ɓangare na yunkurin shugaban ƙasa domin rage wa mutane raɗaɗin cire tallafin mai.
Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja
A wani rahoton na daban Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar APC ta ƙasa zasu sa labule da gwamnonin jam'iyyar yau Laraba.
NWC zata gana da gwamnonin ne a wani yunƙuri na neman goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC bayan murabus ɗin Abdullahi Adamu.
Asali: Legit.ng