Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Manyan Shugabannin Kasashen Afirika Uku

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Manyan Shugabannin Kasashen Afirika Uku

  • Shugaban Najeriya da ƙungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, yana ganawa da manyan shugabannin ƙasashen Afirika uku a fadar shugabanci a Abuja a ranar Talata, 18 ga watan Yuli
  • Shugaba Tinubu ya karɓi baƙuncin Patrice Talon na Jamhuriyar Benin, Umaro Sissoco Embalo na ƙasar Guinea-Bissau, da Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar
  • Dukkanin shugabannin ƙasashen uku tare da Shugaba Tinubu sun shiga ganawar sirri a ofishin shugaban ƙasar

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da shugabannin ƙasashen Afirika uku masu makwabtaka da Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

Takwarorin shugaban ƙasar da suka kawo masa ziyara sun haɗa da Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin, Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau, Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Magana Ta Ƙare, Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya

Shugaba na ganawa da shugabannin kasashen Afirika uku
Shugaba Tinubu tare da sauran shugabannin kasashen Afirika a wajen taron AU Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Har ya zuwa dai lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a bayyana haƙiƙanin dalilin ganawar shugabannin ba.

Sai dai, an yi amanna cewa za su tattauna ne kan bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen Afirika wanda zai basu dama su yi gogayya da sauran manyan ƙasashen duniya irinsu Amurka, Faransa, China, Jamus, Rasha da sauransu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabannin ƙasar waɗanda suka iso fadar shugaban ƙasar da rana, ana sa ran za su tattauna muhimman batutuwan tattalin arziƙi da Shugaba Tinubu, jaridar The Nation ta yi rahoto.

Shugabannin sun iso ne a lokuta mabanbanta inda Shugaba Tinubu ya yi musu maraba a harabar ofishinsa.

An karrama Shugaba Tinubu a taron AU a ƙasar Kenya

A ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli an karrama Shugaba Tinubu da tafi na musamman bayan ya iso harabar ɗakin taron ƙungiyar tarayyar Afirika (AU) a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Abdullahi Adamu Ya Rasa Mukamin Shugabancin APC

Shugaban ƙasar wanda a makonnin da suka wuce aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar ECOWAS, an karrama shi da tafi na musamman.

A ranar Asabar Shugaba Tinubu ya shilla zuwa ƙasar Kenya domin ya halarci taron ƙungiyar AU na tsakiyar shekara karo na biyar.

Sunayen Ministocin Tinubu Za Su Bayyana a Gaban Majalisa

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa Shugaba Tinubu zai aike da sunayen mutanen da zai naɗa ministoci a gwamnatinsa zuwa gaban majalisa.

Shugaban ƙasar dai zai aike da sunayen ne bayan yana kusa da shafe wata biyu akan karagar mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng