Kotu Ta Yankewa Fasto Da Wani Hukuncin Kisa Shekaru 4 Bayan Kashe Dalibar LASU
- An yankewa wani faston Najeriya, Segun Philip, da wani Owolabi Adeeko hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe dalibar jami'ar LASU, Favour Daley-Oladele
- Mai shari'a Christiana Obadina ce ta zartar da hukuncin kimanin shekaru hudu bayan Philip da Adeeko sun aikata laifin a jihar Osun
- Philip da Adeeko sun kashe Daley-Oladele don yin asiri da ita da nufin farfado da kasuwancin mahaifiyar Adeeko
Jihar Osun - Mai shari'a Christiana Obadina ta babbar kotun jihar Osun da ke zama a Ikire, ta ya kewa wani fasto mai shekaru 42, Segun Philip, da Owolabi Adeeko mai shekaru 23 hukuncin kisa ta hanyar rataya kimanin shekaru 4 bayan kashe dalibar ajin karshe ta jami'ar LASU, Favour Daley-Oladele, da nufin yin asiri da ita.
Mummunan al'amarin ya afku ne a watan Disambar 2019 lokacin da Adeeko ya gayyaci Daley-Oladele, wacce yake soyayya da iya zuwa Ikoyi, jihar Osun, jaridar Punch ta rahoto.
Adeeko ya yaudari Daley-Oladele zuwa cocin faston a Ikoyi, inda aka sanya mata kwaya a lemu sannan aka kashe ta da tabarya.
Masu laifin sun binne gawar dalibar ta LASU a wani katon rami da suka tona a cikin harabar cocin bayan sun cire wasu sassan jikinta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Malamin addinin ya yi amfani da sassan jikin marigayiyar wajen hada surkulle domin farfado da kasuwancin mahaifiyar Owolabi wanda ke tafiyar hawainiya a wancan lokacin.
Tawagar masu gabatar da kara a karkashin jagorancin Babban Lauya kuma Babban Sakatarkiyar Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Osun, Misis Adekemi Bello, ta ce Owolabi ya shaida wa yan sanda cewa ya yi amfani da budurwar tasa wajen girkawa mahaifiyarsa abinci na kudin jini.
Da take zartar da hukunci a ranar Litinin 17 ga watan Yuli, Mai shari'a Obadina ta yankewa Philip da Owolabi hukuncin kisa ta hanyar rataya da shekaru 14 a gidan yari na hada kai wajen aikata laifi.
Mahaifiyar Owolabi za ta yi shekaru 2 a gidan kaso
Mai shari'ar ta kuma yankewa mahaifiyar Owolabi mai shekaru 46, Bola hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari kan cin naman mutum.
Allah ya yi wa matar Dahiru Mangal rasuwa
A wani labari na daban, mun ji cewa matar shahararran dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal, ta kwanta dama.
Marigayiya Hajiya Aisha ta rasu a wani asibitin Abuja a yammacin ranar Asabar, 15 ga watan Yuli bayan ta sha jinya.
Asali: Legit.ng