Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Tashi Zuwa N617 a Najeriya

Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Tashi Zuwa N617 a Najeriya

  • Farashin litar man fetur ta ƙara tashi daga N539 zuwa sama da N600 a tsakiyar birnin tarayya Abuja da safiyar Talata, 18 ga watan Yuli, 2023
  • A wata ziyara domin tabbatarwa da aka kai gidan man NPPC a Abuja, an gano cewa kamfamin mai na kasa ya ƙara farashi zuwa N617
  • Har yanzun mahukunta ba su bayyana dalilin wannan ƙari ba amma ana ganin wataƙila yana da alaka da hasashen yan kasuwa cewa lita ka iya kai wa N700

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Rahoton Daily Trust da safiyar Talata, ya tabbatar da cewa farashin litar man fetur a Najeriya ya ƙara tashi zuwa N617 a tsakiyar birnin tarayya Abuja.

Yayin wata ziyara da wakilin jaridar ya kai gidan mai mallakin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da ke Abuja ya tabbatar da cewa farashin ya tashi daga N539 zuwa N617 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Daga Ajiye Mukaminsa a APC, An Jibge Jami’an Tsaro a Gidan Abdullahi Adamu

Farashin litar mai ta ƙara tashi a Najeriya.
Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Tashi Zuwa N617 a Najeriya Hoto: NNPCL
Asali: Facebook

Wani kwastoma na daban wanda ya ƙara tabbatar da wannan ci gaban ga wakilin jaridar Daily Trust, ya shaida cewa, "Tabbas da gaske ne, yanzu na sayi mai kan N617 kowace lita."

Meyasa aka samu ƙari kan farashin a NNPCL?

A halin yanzu ba bu wanda ya san dalilin tashin farashi litar mai ba zato ba tsammani kuma mahukunta ba su ce komai dangane da lamarin ba har kawo yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ana hasashen cewa tsadar man ba zai rasa nasaba da hasashen da 'yan kasuwar mai suka yi a kwanakin baya cewa Litar mai ka iya kai wa N700 nan gaba.

Hukumar kula da harkokin Man Fetur ta Najeriya (NDMPRA) ba ta ce komai ba kan sakon da jaridar ta aike mata don tabbatarwa har zuwa yanzu da muke haɗa muku rahoto.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

Wani mazaunin Abuja, James Arpashe ya shaida wa jaridar Premium Times cewa, "Yanzu na sayi mai kan N617 a kowace lita a yankin cibiyar kasuwanci."

A jihar Ogun kuma farashin litar mai ya tashi zuwa N568 a gidajen man kamfanin NNPCL yayin da masu motoci ke ta fafutukar samun mai.

Meya jawo haka?

Mai magana da yawun kamfanin mai na ƙasa, Garba Deen Muhammad, ya bayyana cewa kamfanin zai yi ƙarin haske kan lamarin nan ba da jima wa ba.

Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Ga Dahiru Mangal da Imam Adigun

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Tinubu ya yi ta'aziyya ga fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal bisa rasuwar matarsa.

Haka nan Tinubu ya jajanta wa babban Malamin addinin Musulunci, Imam Adigun bisa rasuwar mahaifiyarsa ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel