'Yan Sandan Jihar Enugu Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Kashe Kansila

'Yan Sandan Jihar Enugu Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Kashe Kansila

  • Jami’an ‘yan sandan jihar Enugu, sun sanar da kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da kashe wani kansila Nelson Sylvester
  • Makasan sun isa gidan kansilan da misalin karfe 11.30 na daren ranar Lahadi, inda suka bude wuta ba tare da bata lokaci ba
  • A yayin harin, Sylvester ya yi kokarin guduwa zuwa gidajen makwabtansa, sai dai ya rasu daga baya sakamakon harbin da suka yi masa

Enugu - Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama daya daga cikin wadanda ake zargin da kashe Nelson Sylvester, kansilan gundumar Eha-Ulo, da ke karamar hukumar Nsukka ta jihar.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe Sylvester, wanda aka fi sani da Ofunwa, a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke Eha-Alumonah, kamar yadda The Punch ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

'Yan sanda sun kama wani da ake zargi da kashe wani kansila
'Yan sandan Enugu sun cafke wani mutum bisa hannu cikin kisan kansila. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

‘Yan sanda na neman sauran makasan

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ce jami’ansu na farautar sauran wadanda ake zargi da hannu a kisan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ndukwe ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.

Sanarwar ‘yan sandan ta bayyana cewa maharani sun je kauyen Umualoji da ke a Ehalumona karamar hukumar Nsukka, ranar Lahadi 16 ga watan Yuli, da misalin karfe 11.30 na dare, inda suka kashe kansilan da ke wakiltar Eha-Ulo Ehalumona.

Kansilan ya rasu sakamakon harbin da suka yi masa

Mazauna yankin da lamarin ya faru sun bayyana cewa ‘yan bindigar da isarsu gidan kansilan suka bude wuta ba kakkautawa.

An bayyana cewa a lokacin kansila ya yi kokarin guduwa zuwa daya daga cikin gidajen makwabtansa, sai dai ya rasu a can sakamakon harbin da suka yi masa.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

Bayan makasan sun tafi ne mutanen unguwar suka fito inda suka gano gawar kansilan a bayan wani gida da ke unguwar.

The Guardian ta ce mazauna kauyen sun bayyana matukar damuwarsu kan mummunan lamarin, saboda a cewarsu kansilan ya kasance mai taimakon jama’ar yankin.

An kama wata mata bisa laifn kwarawa ‘yar sanda ruwan zafi

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton wata mata mai suna Esther Godwin bisa zargin kwarawa daya daga cikin ma’aikatansu tafasasshen ruwan zafi.

Lamarin dai ya faru ne a karshen makon da ya gabata a kauyen Olofin da ke jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng