Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka Da Rikicin APC

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka Da Rikicin APC

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo babban birnin tarayya Abuja daga ziyarar aiki da ya kai kasar Kenya
  • Shugaban kasar ya dawo kasar ne ana tsaka da rikici a APC yayin da shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya yi murabus
  • Bayan murabus din Adamu, babban sakataren APC na kasa, Iyiola Omisore ma ya bi sahunsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Kenya ana tsaka da tashin hankali a cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

An sanar da dawowar shugaban kasar Najeriya ne a cikin wata wallafa da kungiyar Tinubu/Shettima Media Support (TMS) ta yi a Twitter a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.

Shugaban ksa Tinubu ya dawo daga Kenya
Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka Da Rikicin APC Hoto: @TinubuMediaS
Asali: Twitter

Tinubu ya dawo Najeriya daga Kenya

Kunyiyar ta rubuta a twitter:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito: An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Ya Ke Son Nada Wa Minista Daga Jihar Ogun

"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo daga Kenya bayan ya halarci taron rabin shekara na kungiyar AU."

Shugaban kasa Tinubu ya dawo Najeriya ne a lokacin da jam'iyya mai mulki ta tabbatar da murabus din Abdullahi Adamu daga matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

Sanata Abubakar Kyari, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (Arewa), ya maye gurbin Adamu a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

An rahoto cewa an tilastawa Adamu, wanda ya kasance dan gani kashenin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari murabus daga kujerarsa a jam'iyyar a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli.

Yadda Adamu da Omisore suka yi murabu daga shugabancin APC

A cewar rahotanni da dama, tsohon gwamnan na jihar Nasarawa ya mika wasikar murabus dinsa ga shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

An tattaro cewa Uzodinma ya gabatar da wasikar murabus din ga ofishin shugaban ma'aikatan shugaban kasa Tinubu, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Riko Na Jam'iyyar APC

Hakazalika, babban sakataren jam'iyyar na kasa, Iyiola Omisore, ya yi murabus daga mukaminsa tare da Adamu.

An zargi Adamu da Omisore da gudanar da jam'iyyar ba tare da bin ka'idoji ba, hatta a tsakanin mambobin kwamitin aikin jam'iyyar na kasa.

Ga wallafar a kasa:

Sanata Shehu Sani ya yi martani a kan murabus din Adamu a matsayin shugaban APC na kasa

A gefe guda, mun ji cewa tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu manyan laifuka biyu da suka yi sanadiyar murabus din Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Sani ya ce abu na farko shine lokacin da Adamu ya sanar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar maslaha na APC amma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar shi a tsaka mai wuya kafin babban taron jam'iyyar na kasa a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng