“Ban Damu Da Shekaru Ba”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Saurayinta Mai Karancin Shekaru

“Ban Damu Da Shekaru Ba”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Saurayinta Mai Karancin Shekaru

  • Wata matashiya yar Najeriya ta saki hoton wani matashi a soshiyal midiya, tana mai ikirarin cewa saurayinta ne
  • A cewar matashiyar wacce ta girme shi, mutane na iya fadin duk abun da suke so, amma ita bata damu da banbancin shekaru ba
  • Bidiyoyin soyayyarsu da matashin ya jefa mutane cikin rudani, inda wasu suka ce watakila yaya da kani ne ko kuma uwa da 'da

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata yar Najeriya mai dan shekaru ta haddasa cece-kuce bayan ta baje kolin matashin saurayinta a soshiyal midiya.

Da take yada wani bidiyo dauke da hotunanta da na yaron, matashiyar ta ce bata damu da tazarar shekarun da ke tsakaninsu ba.

Matashiyar ta ce tana matukar son saurayin nata
“Ban Damu Da Shekaru Ba”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Saurayinta Mai Karancin Shekaru Hoto: kim_bog12
Asali: TikTok

A cewarta, a shirye take ta ba shi hakuri sau dubu domin bata shirya rasa shi ba. Bidiyonta ya haifar da rudani, inda wasu ke mamakin ko da gaske saurayinta ne ko kuma kaninta.

Kara karanta wannan

An Tsinci Gawar Wata Budurwa Bayan Sun Shafe Tsawon Dare Da Masoyinta a Dakin Otel

Mutane sun yi musun cewa watakila danta ne. Da take martani, matar ta saki wani bidiyo, tana mai cewa ba za ta taba yin wasa da mutumin da ke sanyata farin ciki ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kara da cewar mutane basa taba rasa abun fadi, amma babu abun da zai hana ta sonsa.

"...Me zai sa na dunga wasa da mutumin da ke bani farin ciki mutane za su fadi albarkacin bakinsu ne kawai kuma ni ban damu ba saurayina ne babu abun da zai hana ni sonsa," ta rubuta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Omowonuola ta ce:

"Idan suka zo suka kama ki yanzu za ki fara cewa wasa ne kawai. Kafin ki ce mun babu ruwana. Sai dai idan mutumin/yaron yana da karamin jiki ne."

Eledumare’sMasterpiece ya ce:

Kara karanta wannan

Cikin minti 2: Matar aure ta koka kan yadda maza ke dirka wa mata ciki a kankanin lokaci

"Kaninta ne, akwai kamanni, kawai sai ku yi ta wahalar da junanku."

Ayoola joel:

"Na rantse babu wanda ya kalli bidiyon nan sama da ni na kalla kamar sau 10.
"Don Allah ku tashe ni daga bacci faaaa mafarki nake yi faaa."

Marley Rey ta ce:

"Yar'uwa kin bata, wannan yaron bai san so ba ko bai shirya kasancewa tare da ke ba, ki dawo hayyacinki."

Dan Najeriya ya koka bayan budurwarsa ta rubuta jadawalin lokutan da za su dunga hada gado

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya saki hoton jadalin lokutan kwanciya da budurwarsa ta rubuta.

Matashin ya ce budurwar ta yi korafi da nuna gajiyawa kan yadda yake yawan nemanta a shimfida don haka ta yi wa tufkar hanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng