Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bindige Basarake Har Lahira a Jihar Imo

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bindige Basarake Har Lahira a Jihar Imo

  • 'Yan bindiga sun halaka Basaraken Nguru da ke ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Wata majiya ta ce da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Litinin ɗin nan maharan suka shiga har fadar sarkin suka aikata haka
  • Hukumar 'yan sanda ta ce tuni kwamishina ya kafa tawagar kwararrun jami'an da zasu gudanar da bincike kan kisan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Imo state - 'Yan bindiga sun harbe basaraken garin Nguru, ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, mai martaba Eze James Nnamdi, har lahira ranar Litinin da yamma.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan bindigan sun kutsa kai har cikin fadar basaraken kuma suka yi ajalinsa da yammacin yau Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023.

Taswirar jihar Imo.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bindige Basarake Har Lahira a Jihar Imo Hoto: punchng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa Marigayi sarkin ya karɓi bakuncin wani mai suna, Chief Ignatius Nwaru, yana tsaka da sauraron bakon lokacin da maharan suka kutsa kai.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An barbi basaraken gargajiya na garin Nguru da ke ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo har lahira da misalin ƙarfe 3:00 na yammaci."
"Basaraken wanda ya fi shahara da Eze Mmirioma ya rasa rayuwarsa ne a fadarsa, abun ba daɗin ji."

Bayanai sun nuna cewa an gaggauta ɗaukar baƙon marigayi Sarkin zuwa Asibiti kuma a halin yanzun yana kwance likitoci na kula da shi domin ceto rayuwarsa.

Wannam hari da ya yi ajalin basaraken ya jefa tashin hankali, fargaba da ɗar-ɗar a zuƙatan mazauna yankin.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya ce tuni kwamishinan 'yan sanda, Muhammed Barde, ya umarci a fara bincike kan kisan.

Kara karanta wannan

Farin Ciki: Sojoji Sun Kama Wasu 'Yan Kasar Waje Da Ke Kokarin Shigo Da Muggan Makamai Cikin Najeriya Maƙare A Mota

Leadership ta rahoto kakakin yan sandan ya ce:

"Kwamishinan yan sandan Imo, Muhammed Barde ya yi Allah wadai da kisan Eze Mmirioma, basarake a yankin Aboh Mbaise, wanda ya rasa ransa a Asibiti bayan harbin da aka masa a gida."
"CP ya kafa tawagar kwararru domin gudanar da bincike kan wannan Kes ɗin da tabbatar da cewa an damƙo duk mai hannu kuma doka ta yi aiki a kansa.

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 6 a Kauyukan Jihar Benuwai

A wani rahoton na daban 'Yan bindiga sun aikata mummunan ta'adi a garuruwa biyu ranar Lahadi da daddare a jihar Benuwai.

Rahoto ya nuna maharan sun halaka rayukan mutum 6 yayin da suka kai farmaki kauyukan da ke ƙaramar hukumar Ushongo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262