Gwamnan Jihar Abiya Ya Bakado Ma'aikatan Bogi Sama da 2,000

Gwamnan Jihar Abiya Ya Bakado Ma'aikatan Bogi Sama da 2,000

  • Gwamnatin jihar Abiya karkashin sabon gwamna, Alex Otti, ta fara aikin bankaɗo badaƙalar bangaren ma'aikata
  • Akanta Janar ta jiha, Njum Onyemenam, ta ce zuwa yanzun an gano ma'aikatan bogi 2,300 kuma an ceto N200m
  • Ta ce wannan aiki zai ci gaba kuma da yiwuwar a sake gano wasu ma'aikatan bogin da ake tura wa albashi duk wata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abia state - Gwamnatin jihar Abiya ta ce ta tseratar da kuɗi kimanin miliyan N200 da ake biyan ma'aikatan bogi a jihar.

Channels tv ta tattaro cewa gwamnatin ta ce ta samu wannan nasara ne bayan gano ma'aikatan ƙarya 2,300 a tsarin biyan albashi yayin tantance sahihan ma'aikata.

Gwamnan Abiya, Alex Otti.
Gwamnan Jihar Abiya Ya Bakado Ma'aikatan Bogi Sama da 2,000 Hoto: Alex Otti

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran mai girma gwamna Alex Otti na jihar Abiya, Kazie Uko, ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Saura Kiris Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kudirin N200k a Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma'aikatan Najeriya

Ya ce Akanta Janar ta jihar, Njum Onyemenam, ta bayyana cewa an gano badakalar ma'aikatan bogin ne ta hanyar biyan albashi da tsari guda ɗaya tal.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma tabbatar da cewa waɗan nan ma'aikatan bogin sun samu albashinsu na watan Afrilu da kuma fanshon watan Yuni.

Mun gano ma'aikatan bogi 2,300 - Onyemenam

Da take ƙarin bayani a wata sanarwa, akanta janar ta ce Gwamnati ta bankaɗo ma'aikata 2,300 na bogi kuma ta ceto kuɗi kimanin miliyan N200m.

Jim kaɗan bayan gana wa da gwamna Otti ranar Litinin, Misis Onyemenam ta ce za a ci gaba aikin tantance wa da bincike kuma da yiwuwar a ƙara bankado wasu ma'aikatan.

Ta ce:

"Mafi karanci mun cire sunayen ma'akatan bogi 2,300 daga tsarin biyan albashi na jiha ta hanyar bin tsari ɗaya wajen biyan albashi, muna fatan ƙara gano wasu nan gaba."

Kara karanta wannan

Biliyan 500 Na Kayan Rage Radadi: Abba Gida-Gida Ya Ce Bai Soki Tinubu Ba

Gwamna Otti ya bada umarnin biyan ma'aikata bashi

Bugu da ƙari, ta yi bayanin cewa bayan umarnin gwamna Otti, gwamnatin Abiya ta biya albashin watan Afrilu da tsohuwar gwamnati ta bar mata da kuma kuɗin yan Fansho na watan Yuni.

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

A wani rahoton na daban Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da sakataren jam'iya, Iyiola Omisore, sun sauka daga muƙamansu.

Kwamitin gudanarwar APC (NWC) ne ya tabbatar da murabus ɗin Adamu da Omisore ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262