Majalisar Dokokin Jihar Osun Ta Canja Sunan Jihar, Ya Koma Na Asali
- Majalisar dokokin jihar Osun ta amince da kudirin sauya sunan jihar ya koma na asali kafin abinda ya faru a 2012
- A zamanin mulkin tsohon gwamna Rauf Aregbesola, aka sauya sunan daga 'Osun State' ya koma 'State of Osun' a 2012
- Sai dai bayan amincewa da kudin yau Litinin, majalisar ta maida sunan ya koma na asali watau "Osun State' ta kuma yi wasu sauye-sauye
Osun - Majalisar dokokin jihar Osun ta amince da kudirin sauya sunan jihar Osun daga, "State Of Osun" a yanzun ya koma asalin yadda kowa ya sani watau 'Osun State.'
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an canza sunan jihar Osun daga asalinsa zuwa 'State of Osun' a shekarar 2012 lokacin mulkin tsohon gwamna, Rauf Aregbesola.
Amma a zaman ranar Litinin, majalisar dokokin ta hanyar kudiri "Garambawul ga take da tutar jihar Osun" ta canja sunan zuwa asalin jihar watau 'Osun State.'
Bayan kudurin ya tsallake karatu na uku, shugaban majalisar dokokin jihar, Honorabul Adewale Egbedun ya ce zasu tura kudirin ga mai girma gwamna domin ya rattaɓa hannu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce da zaran mai girma gwamna ya rattaɓa hannun kan kudirin, zai maye gurbin kudirin take da tutar jihar Osun 2012.
Abubuwan da kudirin ya ƙunsa
Jaridar The Nation ta rahoto cewa baya ga sauya sunan jihar, kudirin ya kuma sauya tutar jihar Osun ta koma tutar Najeriya da kuma ta alamar rundunar tsaron ƙasar nan.
Sai kuma taken jihar Osun da ke ƙunshe a tsohon kudirin, shi kaɗai ne gyaran bai taɓa ba, taken na nan yadda yake a baya.
Majalisar ta fara aikin tantance kwamishinoni
Bayan haka ne majalisar ta tantance 13 daga cikin jerin kwamishinoni 25, waɗanda suka bayyana gabanta bayan kafa kwamitin wucin gadi.
Shugaban kwamitin, Mista Akinyode Oyewusi, yayin da yake bada shawarai, ya ce baki ɗaya mutanen sun cancanta kuma suna da gogewar zama kwamishinoni.
APC Ta Tabbatar da Adamu da Omisore Sun Yi Murabus Daga Mukamansu
A wani rahoton na daban Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu da sakataren jam'iya, Iyiola Omisore, sun yi murabus daga kan muƙamansu.
Mukaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da lamarin yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron NWC a Abuja.
Asali: Legit.ng