Gardamar Shinkafa Ta Jawo Yaron Gida ya Kashe Malami da Tabarya Cikin Dare
- Mai aiki ya yi sanadiyyar mutuwar ubangidansa saboda sun samu sabani wajen dafa masa shinkafa
- Yanzu haka ana zaman makokin Chima Anolue wanda malami ne a jami’ar tarayya ta Nnamdi Azikiwe
- ‘Yan bangan Anambra su ka ragargaji wanda ake zargi sai da ya fada masu gaskiyar abin da ya faru
Anambra - Chima Anolue malami ne a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke garin Awka a jihar Anambra, ya gamu da ajalinsa a hannun wani yaron gidansa.
Daily Trust ta ce Chima Anolue wanda ke koyarwa a sashen kula da tunanin mutane ya samu mummunan sabani a daren Asabar da mai yi masa aiki.
Ana zargin Marigayin ya tasa yaron a gaba saboda ya kyale shinkafa ta kone a wuta, wautar mai aikin ce ta jawo malamin jami’ar ya shara masa mari.
Magana ta fito daga baya
Da farko dai yaron ya musanya cewa shi ya yi sanadiyyar kisan, da ya ji matsa a hannun ‘yan banga, sai aka ji ya amsa aikata wannan danyen aiki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wani fai-fan bidiyo a Facebook, wanda ake zargi ya nuna shinkafa ce ta jawo ya yi kisan.
Abin da wanda ake zargi ya fada
"A lokacin da ya dawo, sai ya fada mani in dafa shinkafa. Ina cikin dafa shinkafar, sai ya tambaye ni ko mai ya hana ni wanke kwanoni.
Ban ce masa uffan ba, sai ya fara tambaya ko meyasa ba na ba shi amsa. Ana haka sai ya mare ni.
Na fada masa ina yawon samun matsalar kunne, kuma mutane ba su mari na, ina fadan haka sai ya fusata saboda ina maida masa magana.
Saboda haka sai ya sake shara mani mari, ya kuma dauko bulala ya rika sharba mani a ko ina.
A sanadiyyar haka na ji haushi, mu ka fara fada. A wajen fadan ne na dauko tabarya a dakin dafa abinci, sai na rankwala masa a kansa.
- Wanda ake zargi
Bayanin da aka samu daga shafin Linda Ikeji ya ce abin ya faru ne kauyen Ifite a Akwa, ko da aka tafi asibiti a gurguje, sai aka ji Anolue ya mutu.
'Yan bindiga a cikin mahajatta?
Mutanen gari sun ankarar da hukuma da aka ji kishin-kishin Bello Turji zai tafi Saudi Arabiya, rahoto ya nuna hakan ya sa aka fara binciken mahajjata.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun tafi kasa mai tsarki daga Tsafe, Zurmi, Bungudu da Shinkafi, su na isowa filin jirgin Najeriya, aka cafke su.
Asali: Legit.ng