FUNAAB Ce Babbar Jami’a Ta Biyu da Ta Fi Kowacce Nagarta a Najeriya, Bayanai Sun Bayyana

FUNAAB Ce Babbar Jami’a Ta Biyu da Ta Fi Kowacce Nagarta a Najeriya, Bayanai Sun Bayyana

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, daya daga cikin jami’o’in Najeriya ta samu shiga jerin fitattu a Afrika
  • Yanzu haka, an ce jami’ar FUNAAB ce ta biyu mafi nagarta a Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana
  • Hakazalika, jami’ar wacce ke a jihar Ogun ita ce ta 26 a jerin jami’o’i mafi nagarta a yankin Saharar Afrika

Jihar Ogun - Jami'ar Aikin Gona ta Tarayya, Abeokuta (FUNAAB) ta zama ta biyu mafi nagarta a cikin jami'o'in Najeriya 258 kuma ta 26 mafi nagarta a yankin Saharar Afirka.

Wannan na zuwa a cikin wata rahoton da aka fitar kwanan nan da kafar Times Higher Education's (THE) ke tattarawa, The Guardian ta ruwaito.

Kididdigar ta bayyana manyan jami'o'i mafi tasiri a Afirka duba da ma'auni na wasu ginshikai biyar, wato samun dama da adalci; tasirantuwa a Afirka; basirar koyarwa; damawa da dalibai da kuma albarkatu da ma kudi.

Kara karanta wannan

2023: Jami'o'in Najeriya 10 Mafi Nagarta, Jami'ar Arewacin Najeriya Ta Samu Shiga

Jami'a ta biyu mafi nagarta a Najeriya
Wannan wani yanki ne na cikin jami'ar FUNAAB | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda lamarin yake

A ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023 ne aka sanar da matsayin jami'o'in yankin kudu da hamadar Sahara a hukumance a taron farko na kungiyar, wanda ya gudana tare da hadin gwiwar jami'ar Ashesi da ke Ghana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kididdigar, wacce aka samar tare da haɗin gwiwar gidauniyar Mastercard, ta ba da matsayin jami'o'i 88 daga kasashe 17 na yankin, Business Day ta tattaro.

Martanin jami’ar FUNAAB

Shugaban FUNAAB, Farfesa Olusola Babatunde Kehinde, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya taya daukacin al’ummar jami’ar murnar wannan gagarumin nasara.

Ya kuma bayyana fatan cewa, nasarar za ta taimaka wajen kara kwazo wajen gudanar da ayyukan ma’aikata da gwazon kaimin karatu ga daliba.

Najeriya ce dai uwa a Afrika, amma duk da haka akan samu lokacin da wasu kasashen mata fintikau a bangarori da yawa.

Kara karanta wannan

Rikici: An kama motar shugaban APC a jihar Arewa, an titsie direbansa kan wani batu

Jerin jami'o'in Najeriya 10 da suka fi inganci a 2023, jami'ar Umaru Musa Yar'adua na ciki

A wani rahoton, mujallar The Times Higher Education (THE) ta sanar da jerin jami'o'in Nahiyar Afirka da suka yi fice.

Jadawalin jerin sunayen jami'o'in na 2023 an fitar da su ne bayan nazari da duba yadda suke kawo maslaha a matsalolin da suka addaban yankin.

Daga cikin jerin sunayen jami'o'in akwai na Najeriya 30 da suka samu fitowa. Jami'ar Covenant da ke jihar Ogun ita ce ta daya a Najeriya, yayin da ta kasance ta 7 a Nahiyar Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.