'Yan Sanda da Hadin Bakin Gwamnatin Zamfara, Sun Kame Motar Shugaban APC, Sun Tsare Direbansa

'Yan Sanda da Hadin Bakin Gwamnatin Zamfara, Sun Kame Motar Shugaban APC, Sun Tsare Direbansa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu ‘yan sanda sun kama motar shugaban jam’iyyar APC a jihar Zamfara
  • Jam’iyyar na zargin gwamnatin jihar da kuma ‘yan sanda da kokarin musgunawa ‘ya’yanta saboda wasu dalilai
  • Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun ce basu san da faruwar lamarin ba, sai dai suna bincike don gano tushen matsalar

Jihar Zamfara - Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zargi rundunar ‘yan sandan jihar da gwamnatin jihar da kwace motar shugabanta, Tukur Danfulani daga hannun direbansa a Gusau babban birnin jihar.

Bakar motar kirar Hilux mai lamba GUS 51 AH a cewar jam’iyyar APC, wasu ‘yan sanda da ake zargin suna da alaka da gwamnati ne suka kama ta ba tare da wani sammacin doka ba.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa, an kuma tsare direban na sa’o’i da dama ba tare da yi masa tambayoyin abin da ake zarginsa akai ba idan akwai, TVC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ka ji tausayi: Yadda fasto ya tara dandazon jama'a suka yi girki a sansanin gudun hijira

Yadda 'yan sanda suka kama motar shugaban APC a jihar Zamfara
Wannan ne motar da ake zargin 'yan sanda sun kwace | Hoto: tvcnews.tv
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun APC, Yusuf Idris, jam’iyyar ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, sannan ta bukaci a dawo da motar cikin gaggawa tare da neman gafara a rubuce daga bangarorin da abin ya shafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da APC ta zargi ake shirin yi mata a Zamfara

Yusuf ya ce jam’iyyar APC ta yi imanin cewa, abin da ya faru wata mnufa ce ta ‘yan sanda da gwamnatin jihar na yin barazana ga mambobinsu da shugaban jam’iyyar.

Babbar jam’iyyar adawar a Zamfara ta dage cewa wannan ba lamari bane da za ta lamunta don ana ci gaba da yiwa mambobinta barazana.

Hakazalika, Yusuf Idris ya ce rayuwar shugaban jam’iyyar APC na Zamfara, Tukur Danfulani da ta iyalansa na fuskantar barazana, yayin da ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sanya ido.

Kara karanta wannan

Badakalar N1bn: Kotu Ta Bayar Da Sabon Umarni a Shari'ar Tsohon Kwamishinan Ganduje

Da yake mayar da martani kan zargin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma ya bayar da tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan za ta yi bincike tare da gano jami’an da ke da hannu a batun.

Da musguna mana aka fara

A bangare guda, Legit Hausa ta tattauna da wani mamban jam’iyyar APC a jihar Zamfara kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, inda ya bayyana yadda APC ke fuskantar matsala.

A cewar Ishaq Adamu Muhammad, tun farko dama da musgunawa APC aka fara mulki a jihar ta Zamfara.

A cewarsa:

“Da mugun nufi suka fara mulki, don haka za su yi abin da ya fi haka ba. Saboda tsohon gwamna Matawalle aka fara muzantawa duk da kokarin da ya yi a jihar nan.”

A watan Yunin da ya gabata ne aka samu cece-kuce da rikici game da kwace motocin tsohon gwamnan Zamfara Matawalle da 'yan sanda suka yi.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Wata Likita Bayan Yin Basaja A Matsayin Marasa Lafiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.