Yadda Fasto Ya Kirkiri Taron Dafa Abinci, Ya Taimakawa ’Yan Gudun Hijira a Jihar Benue

Yadda Fasto Ya Kirkiri Taron Dafa Abinci, Ya Taimakawa ’Yan Gudun Hijira a Jihar Benue

  • Yayin da yunwa ke ci gaba da kwakwular jama’a, wani malamin coci ya yi abin a yaba da yi masa addu’ar fatan alheri
  • An ruwaito yadda ya tara dandazon jama’a domin gudanar da taron dafa abinci a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Benue
  • Ya zuwa yanzu, mutane na ci gaba da martani mai daukar hankali kan abin da wannan faston ya aikata na alheri

Dauda, jihar Benue - Ana ci gaba da gudanar da taron dafa abinci da Rabaran Solomon Mfa ya shirya a sansanin ‘yan gudun hijira na jihar Benue domin ciyar da ‘yan gudun hijira.

A cewar majiya, an shirya taron ne da nufin rage radadin yunwa ga mutanen da rashin tsaro ya raba da gidajensu.

Yadda Fasto ya ba da gudunmawa a girki
Fasto ya kirkiri taron dafa abinci a jihar Benue, ga lokacin da ake girkin | Hoto: Shakyum Joseph Kayode
Asali: Facebook

Wani mai amfani da kafar Facebook wanda ya uyada hotunan ya ce:

Kara karanta wannan

Kudi sirri ne: Bidiyon mai bidiyon bakwanci Mark Angel ya tada hankalin jama'a

"BENUE IDP COOK-A-THON. Kai tsaye daga yankin Dauda na Benue, inda ake gudanar taron dafa abinci don karya yunwa a sansanin ‘yan gudun hijira.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ku yi tunani a ce akwai irin Fr Mfa 10 a Benue. Allah ya yiwa wannan mutumin albarka."

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Bayan da kafar yada labarai ta Punch ta yada hotunan daga baya, mutane da yawa sun yi martani bisa abin da malamin na coci ya aikata. Ga kadan daga ciki:

Wilson Ifeoma:

“Allah ya kara maka albarka Baba, karin aikin alheri, hikima, ilimi da fahimta cikin sunan Yesu mai girma Amin .”

Tochukwu Jidere:

“Allah ya saka maka da alkhairi bias wannan aiki na alheri da aka yiwa marasa karfi... la dace a yi koyi da kai.”

Cheche Laz page:

"Allah ya maka albarka, kariyarsa ta cigaba da sambada a kanka har abada ."

Kara karanta wannan

“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo

Ismail Adesina Abubakar Alaro:

"Allah ya karbi kyakkyawan aikinka, ka ci gaba da yiwa al'umma hidima."

Yana Xtiano Chia:

"Allah ya saka maka da alkhairi Baba da duk wanda ya bada gudunmawa ta wata hanya ❤️."

Mata ta gina gidaje 2 ba tare da mijinta ya sani ba, kuma ta mare shi sadda da ya tambayi dalili

A wani labarin, wata matar aure ta gina gidaje biyu ba tare da ta sanar da mijinta game da yadda ta samu damar yin ginin ba.

A wani labari da @Postsubman ya wallafa a shafin Twitter, mutumin ya ce lokacin da ya tambayi matarsa abin da ta yi, sai kawai ta kafta masa mari.

Da yake ba da labarin, mutumin ya ce matarsa ta yi amfani da sunayen ‘ya’yansu biyu ne a lokacin da ta yi rajistar gidajen biyu da ta gina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.