Mata Ta Gina Gidaje 2 Ba Tare da Mijinta Ya Sani Ba, Kuma Ta Mare Shi Sadda da Ya Tambayi Dalili

Mata Ta Gina Gidaje 2 Ba Tare da Mijinta Ya Sani Ba, Kuma Ta Mare Shi Sadda da Ya Tambayi Dalili

  • Wata matar aure ta kammala aikin gina gidajenta manya guda biyu a asirce ba tare da sanar da mijinta ba
  • Mutumin ya ce matarsa ta gina gidajen tsaf kuma ta yi rajista da sunayen ‘ya’yansa biyu da suka haifa tare da ita
  • Ya koka da cewa lokacin da ya fuskanci matarsa game da abin da ta yi, sai ta tada hankali ta mare shi a madadin yi masa bayani

Wata matar aure ta gina gidaje biyu ba tare da ta sanar da mijinta game da yadda ta samu damar yin ginin ba.

A wani labari da @Postsubman ya wallafa a shafin Twitter, mutumin ya ce lokacin da ya tambayi matarsa abin da ta yi, sai kawai ta kafta masa mari.

Da yake ba da labarin, mutumin ya ce matarsa ta yi amfani da sunayen ‘ya’yansu biyu ne a lokacin da ta yi rajistar gidajen biyu da ta gina.

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Jurewa Ba”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Jadawalin 'Hada Shimfida' Da Budurwarsa Ta Rubuta Masa a Bidiyo

Yadda mata da miji suka samu sabani
Hotunan nan ba na mata da mijin bane, an saka su ne don buga misali | Hoto: Getty Images/AlexanderFord and Vladimir Vladimirov.
Asali: UGC

Daliln da yasa ta yi masa haka

Daya daga cikin dalilan da ya sa matar ta yi abin da ta yi shi ne ta bata wa mijinta rai, wanda ta ce ya dirka wa wata mata ciki a shekarun baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai mutumin ya ce matarsa ta yafe masa tuni, kuma sun daidaita tsakaninsu kan batun uiwa wata mata ciki.

Amma ga dukkan alamu ita dai matar tana rike da batun, kuma kudin da ta gina gidajen nata ne. Mutumin ya ce matarsa ta ma samu karin girma a wurin aiki, kuma bai sani ba.

Ga abin da yake cewa

A kalamansa:

"Na fusata sannan na yi kokarin kwace mukullin motarta a zazzafar rigimar da muke, ita kuma ta mare ni.
“Wannan abu ya ba ni mamaki, na shirya wata ‘yar jaka ta, kuma na yi sati guda bana gida. Tunanin ita ce matar da na kai makaranta kuma na yi abubuwa da yawa a kanta, kuma ta saka min da wannan butulcin.”

Kara karanta wannan

"Ya Daina Cin Abinci Na": Matar Aure Ta Bari Garjejen Kato Ya Yi Mata Tausa, Mijinta Ya Fusata Matuka

Martanin jama’a

Bayan ganin abin da ya faru, jama’a da yawa a kafar sada zumunta sun yi martani kamar haka:

@Adonisee ya ce:

"Ka banka wa wata ciki ba tare da aure ba kuma har kana da bakin rigima? Da ace ka tsarkake rayuwar aurenku za ka rasa kimarka ne? Haba idan ka kama ta da wani namiji ko ka gane wani ya banka mata ciki, za ka yafemata ne?"

@unyimeu60018288 ya ce:

"Jajircewa, ahahahahaah, ka dirka wa yarinya ciki ba tare da aure ba kuma har yanzu ka ke tsammanin amana daga matarka...abin dariya...wato matar nan ta ci gaba."

Yadda maza suka banbanta da mata wajen haihuwa

Wata mata farar fata da ta auri wani dan Najeriya ta tayar cece-kuce da kalamanta masu daukar hankali game da daukar ciki da mata ke yi.

A cikin wani faifan bidiyo da @h.kstory ta yada a TikTok, matar ta ce tsawon mintuna biyu kadai ake dauka mata su dauki ciki, amma sai su yi ta dakonsa na tsawon watanni tara.

Kara karanta wannan

“Kaina Ya Kulle”: Budurwa Ta Shiga Rudani Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta

Matar da ke da juna biyu a halin yanzu ta nuna katon cikinta a yawancin faifan bidiyo ta yada a shafinta na TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.