“Tana Bukatar Tausa Akai-Akai”: Jama’a Sun Yi Martani Kan Bidiyon Yar Shekaru 4 Da Ta Kware a Kitso

“Tana Bukatar Tausa Akai-Akai”: Jama’a Sun Yi Martani Kan Bidiyon Yar Shekaru 4 Da Ta Kware a Kitso

  • Bidiyon wata karamar yarinya da Allah ya horewa baiwar iya kitso ya yadu a soshiyal midiya kuma ya burge mutane da dama
  • A bidiyon, an gano yarinyar mai shekaru 4 tana kitsa gashin kan wata mata cike da kwarewa
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon wanda tuni ya karade duniyar soshiyal midiya

Duk da cewar akwai wasu manya da basu iya kitso ba, wata karamar yarinya ta tabbatar da cewar ba lallai sai manya kadai bane za su iya yin wasu abubuwa yara ma na iya yi.

Karamar yarinya tana kitso
“Tana Bukatar Tausa Akai-Akai”: Jama’a Sun Yi Martani Kan Bidiyon Yar Shekaru 4 Da Ta Kware a Kitso Hoto: @9jabraider
Asali: Instagram

Wata mai shafin kitse-kitse, 9jabraider ta wallafa bidiyon wata yarinya da aka ce shekarunta 4 tana kitsa gashin kan wata mata.

A bidiyon da ya yadu a yanzu, an gano yarinyar tana kitsa kan matar cike da kwarewa ba tare da wani tangarda ba.

Kara karanta wannan

Zololo kenan: Mata mai tsawon da ya kusan taba 'ceiling' ta dauki hankalin jama'a

Yanayin yadda take kitsa kan cikin sauri ya nuna cewa ta kware sosai a harkar kitso.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

trinirumandwhisky:

"Na fara ina shekar 6 kuma na zama kwararriya a shekaru 8. Ina zaune a kasar waje kuma ywancin yaran suna iya kitso tun suna kananan yara. Allah ya albarkaci wannan kyakkyawan hannu na yar shekaru 4. Za ta yi nisa a rayuwa."

kpoguemauricette:

"Na ji kunya ko tsaga kitso ban iya ba."

holistic.airi:

"Kuma yar yarinya na bukatar a dunga yi ma hannun tausa akai-0akai. A kula da wadannan hannaye masu albarka."

ovamedspa:

"Ta kusa shiga kundin bajinta na Guinness."

gmacs4: "

"Kada a kuskura ta rasa kudi a hannu."

kelly_06.24.19:

"Ina fatan ba za su bari kitso ya janye yarintarta ba."

Kara karanta wannan

“Ina Iyayensu Suke?”: Bidiyon Wani Matashin Yaro Da Yar Yarinya a Otel Ya Girgiza Intanet

Budurwa ta cika da farin ciki bayan ta gwangwaje kanta da dan karamin gida, bidiyon ya yadu

A wani labari na daban, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 19 ta garzaya dandalin sadarwar zamani domin nunawa duniya babban nasara da ta samu a rayuwa a cikin wannan mataki da ta ke kai.

Matashiyar ta baje kolin dan karamin gidan kwano da ta ginawa kanta sannan ta bayyana cewa tana matukar alfahari da hakan ba tare da damuwa da abun da mutane za su ce a kan gidan nata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng