“Na Shiga Uku”: Matashi Ya Saki Jadawalin ‘Sharadin Kwanciya’ Da Budurwarsa Ta Rubuta

“Na Shiga Uku”: Matashi Ya Saki Jadawalin ‘Sharadin Kwanciya’ Da Budurwarsa Ta Rubuta

  • Wani matashi dan Najeriya ya wallafa wani bidiyo da ke nuna jadawalin hada shimfida da budurwarsa ta rubuta masa a soshiyal midiya
  • A cewarsa, budurwar tasa ta yi korafi game da yawan bukatuwa da ita da yake yi
  • A wani yunkuri na samun mafita, sai ta fito da wani jadawali don magance lamarin wanda bai yi masa dadi ba

Wani matashi dan Najeriya ya ja hankali yan uwansa yan Najeriya bayan da budurwarsa ta rubuta masu wani jadawali na lokutan da za su dunga kwanciya da juna.

Ya tuna cewa budurwarsa ta yi korafi game da yadda yake son kwanciya da ita sannan ta yi masa gargadin cewa ita a za ta iya ci gaba a haka ba.

Matashi ya saki hoton sharadin kwanciya da ta gindaya masa
“Na Shiga Uku”: Matashi Ya Saki Jadawalin ‘Lokacin Sharholiya’ Da Budurwarsa Ta Rubuta Hoto: @instablog9ja/Instagram, wilpunt/ Getty Images
Asali: UGC

Matar ta kai ga rubuta wani jadawali domin yi wa tufkar hanci kan lamarin wanda ke ci mata tuwo a kwarya.

Kara karanta wannan

"Kana Bin Sa’ar Uwarka”: Uba Ya Kama Dansa Mai Shekaru 21 a Gidan Hajiyar Birni, Bidiyon Ya Yadu

A jadawalin, ta jero ranakun da ta yarda ya taba ta da kuma tsawon lokacin da za su dauka suna sharholiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take wallafa bidiyon, saurayin nata wanda ya karaya ya jaddada cewar ba zai sanya hannu kan yarjejeniyar ba saboda abun ba zai yi masa ta dadi ba.

"A watan Satumban nan, mutanen Najeriya gaba daya azumi ne, ku kalla fa, azumi ne da addu'o'i, babu komai, sai a ranar 12 yanzu, ta ce za ta bari na dandana kadan na mintuna 30.
"Dubi manaja, ita ce manaja, ta sanya hannu, ni yanzu da nake saurayin na sanya nawa hannun. Baaba ba zan iya sanya hannu kan irin wannan takardar da zai jefani a matsala ba faaaa."

Jama'a sun yi martani

@_goofybae_:

"Kun mayar da kwanciyar kafin aure a matsayin ba komai ba yanzu?"

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta a Cikin Bidiyo

@tosinjuls ta rubuta:

"Ku yi aure mana sannan ka samu damar yi mara iyaka, ka daina amfani da na gwaji."

@micheal_x ya yi martani:

"Kamar dai ni kadai ne bana zina a kasar nan."

@lovelyness_ ta ce:

"Wannan awa 2 ka rarraba shi zuwa mintuna 15, kana iya samun karin kwanaki."

@_oluyemisi ta rubuta:

"Wato saurayi da budurwa suna kwanciyar sharholiya."

Matashi na so ayi wa diyarsa gwajin DNA saboda ta yi kama da ogan matarsa

A wani labari na daban, wani dan Najeriya ya bukaci ayi gwajin DNA bayan ya gano cewa diyarsa na kama da ogan matarsa sosai.

Rigima ya fara ne bayan mutumin ya ziyarci wajen aikin matarsa sannan ya hadu da oganta a karo na farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng