Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamiti Yayin da Tinubu Ke Shirin Maye Gurbin Shugabannin Hukumomi Da Aka Rushe

Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamiti Yayin da Tinubu Ke Shirin Maye Gurbin Shugabannin Hukumomi Da Aka Rushe

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shugaban ma'aikatansa, Femi Gbajabiamila, domin ya jagoranci wani kwamiti na musamman da ke da alhakin cike gurbin nada-naden da aka rusa
  • Aikin kwamitin shine kafa tsarin zabar wadanda za a ba mukamai daidai da tanadin doka da cancantar wadanda za a nada a hukumomin gwamnati
  • Sauran mambobin kwamitin sun hada da SGF, George Akume, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci, Mallam Yau Darzo

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shugaban ma'aikatansa, Femi Gbajabiamila, domin ya jagoranci wani kwamiti na musamman da aka daurawa alhakin cike gurbin shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da aka rushe.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, kwamitin da shugaban kasar ya kafa shine ke da alhakin kafa tsarin zaben wadanda za a nada a mukaman daidai da tanadin doka da cancantar wadanda za a nada a Ma'aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Wanda Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministan Kudi

Tinubu na shirin nada sabbin mukamai
Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamiti Yayin da Tinubu Ke Shirin Maye Gurbin Nade-Naden Da Aka Rushe Hoto:@femigbaja
Asali: Twitter

Jaridar ta ambaci wata majiya tana cewa Shugaban kasa Tinubu ya daurawa kwamitin da Gbajabiamila ke jagoranta alhakin fahimtar hukumomin wadanda dokar kafa su ta tanadi ainahin matakin karatu da sai mutum ya kai domin darewa matsayin.

Nade-naden hukumomin gwamnati: SGF George Akume, da wasu za su yi aiki tare da Gbajabiamila

Legit.ng ta tattaro cewa sauran mambobin kwamitin na musamman sun hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci, Mallam Yau Darzo da wasu masana harkokin shari'a da kamfanoni masu zaman kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa a kwanaki ne shugaban kasar ya sanar da rushe shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, sai dai abun bai shafi wasu hukumomin ba.

Tinubu na iya nada wani tsohon shugaban banki daga kudu maso yamma a matsayin ministan kudi, majiya

Kara karanta wannan

Jerin Shahararrun Yan Siyasa Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da yan Najeriya ke jiran jerin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu, wani rahoto ya yi nuni ga wanda za a iya nadawa a matsayin ministan kudi.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, mutumin da ake tunanin baiwa wannan mukami na minista ya kasance wani tsohon shugaban wani bankin zamani daga kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng