Matar Aure Ta Tona Asirin Kanta, Ta Faɗi Yadda Ta Rika Samun Ciki Duk da Mijinta Juya Ne
- Wata matar aure ta bayyana gaskiya mai ɗaga hankali, ta ce mijinta ba shi ne asalin uban 'ya'yan da ta haifa a gidansa ba
- A wani saƙo da ya fasu a shafin Facebook, matar ta ce mijinta ya zo ya gaya mata cewa ya ɗirka wa wata mace ciki a waje
- Sai dai ta ce hakan ba zai taɓa yiwuwa ba saboda tuntuni ta san cewa mijinta juya ne ba zai iya yi wa mace ciki ba
Wata yar Najeriya ta bayyana cewa bayan ɗaura mata aure da wanda take so, ta gano cewa mijinta rago ne a gado ba zai iya yi wa mace ciki ba saboda juya ne.
Maimakon ta ɗaga murya ko ta riƙa sakin maganganu kan lalurar abokin rayuwarta, sai ta yi gum da bakinta kuma ta ci gaba da zama da Angonta.
"Ya Daina Cin Abinci Na": Matar Aure Ta Bari Garjejen Kato Ya Yi Mata Tausa, Mijinta Ya Fusata Matuka
Matar ta riƙa fita waje tana neman maza suna ɗirka mata ciki kuma ta dawo ta haifi ya'ya da sunan na mijin ne, shi kuma yana ɗaukar ɗawainiyarsu ba tare da ya san komai ba.
Taya matar take zuwa ta ɗauko cikin wasu mazan duk da tana da aure?
A wani saƙo da ya fasu a shafin Facebook, matar ta bayyana cewa mijinta bai san cewa dukkan 'ya'yan da yake bugun ƙirjin nasa ne, ba shi ne ubansu na gaskiya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce wata rana mijin ya dawo gida sai ya faɗa mata cewa an samu matsala ya yi wa wata mace ciki a waje kuma ya nemi ta yafe masa.
Ta ce matar da mijinta ya yi wa cikin ta masa barazana, ta nemi ya bata kuɗi kuma ya biya mata kuɗi ta bar ƙasar nan idan yana son ta rufa masa asiri.
Bayan Shafe Shekaru 10 Ba Miji, 'Yar Najeriya Ta Sace Zuciyar Santalelen Bature, Ana Gab Da Aurensu Yanzu
Matar ta bayyana cewa mijinta juya ne
Matar ta ƙara da cewa ta yi mamakin jin haka saboda ta san mijin ba zai iya yi wa mace ciki ba domin juya ne.
A sakon da ya watsu a Facebook, matar ta ce:
"A halin yanzu na rasa yadda zan yi na gaya wa mijina cewa wannan matar makaryaciya ce, ina da yaƙinin cewa mijina juya ne. Ina tsoron aure na ya mutu saboda zai gane yaran da muka haifa ba nasa bane."
"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Durkusa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci
A wani labarin na daban kuma Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.
Magidancin ya gaya mata cewa shi ɗan gargajiya ne kuma ya zama dole ta duƙa kan guiwowinta idan zata ba shi abinci.
Kyakkyawar Baturiya Na Neman Mijin Aure Ido Rufe, Za Ta Bayar Da Makudan Kudi Ga Duk Wanda Ya Samo Mata Miji
Asali: Legit.ng