Dokar Zaman Gida: Muna Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litinin, Gwamna Mbah

Dokar Zaman Gida: Muna Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litinin, Gwamna Mbah

  • Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya ce jiharsa na tafka asarar kuɗi biliyan N10bn a duk ranar Litinin ta kowace mako
  • Mbah, mamban jam'iyyar PDP ya ce Enugu na rasa waɗan nan kuɗin ne sakamakon dokar zaman gidan da IPOB ta ƙaƙaba
  • Ya ce babu wata dokar zaman gida, ya kamata mutane sun fahimci cewa bai kamata su na yi wa wasu tsirarun mutane biyayya ba

Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce dokar zaman gidan da ƙungiyar 'yan aware IPOB ta ƙaƙaba a Kudu maso Gabas, tana jawa jiharsa asarar makudan kuɗaɗe.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa a kowace ranar Litini da dokar ke aiki, jihar Enugu na tafka asarar kuɗi kimanin biliyan N10bn, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Gwamnan Legas da Wani Gwamnan Arewa a Villa

Gwamnan Enugu, Peter Mbah.
Dokar Zaman Gida: Muna Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litinin, Gwamna Mbah Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Asali: Facebook

Peter Mbah ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Enugu a wurin taronsa da shugabannin garuruwan da ke cin gashin kansu.

Ya ce jihar na asarar wannan makudan kuɗin ne sakamakon hana gudanar da harkokin kasuwanci da tattalin arziƙi a kowace ranar Litinin saboda haramtacciyar dokar zaman gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa:

"Yana da amfani mu san dangantakar talauci da wannan dokar da ake kira zaman gida. Duk ranar Litinin din da muka zauna a gida muna rasa N10bn saboda hana harkokin arziki a nan jihar mu."
"Duk mutanen da suka zauna a ɗakunan Otal-Otal da niyyar sai ranar Litinin zasu tafi, yanzu dole su ke sauya shawara ba zasu wuce ranar Lahadi ba, me ya faru kenan? Masu Otal sun rasa kuɗin shigar da zasu samu a ranar."
"Haka nan mutanen da ya kamata su zo Enugu domin harkokin tattalin arziki da kasuwanci, a yanzu ba zasu yi gigin zuwa ba saboda kun ce zaman gida kuke yi duk ranar Litinin."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Babban Sarki da Tawagarsa a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

Ya kamata mutane su fahimci babu wata dokar zaman gida - Mbah

A cewarsa, tabarɓarewar tsaro da dokar zaman gida ka iya kawo wa kudirinsa na inganta tattalin arzikin jihar Enugu cikas.

Gwamna Mbah ya roki shugabannin da su koma su ja hankalin mutanensu kuma su fahimtar da su cewa babu wata dokar zaman gida ranar Litinin ko wata rana daban.

Mbah ya tabbatar wa al'umma cewa hukumomin tsaro suna da bayanin komai, zasu tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mutanen Enugu.

Wani Shaida da PDP Ta Gabatar Ya Bata Kunya a Gaban Kotu, Ya Bayyana Gaskiya

A wani labarin na daban kuma An yi wata dirama a Kotun zabe yayin da jam'iyyar PDP ta gabatar da wani shaida ranar Jumu'a.

Shaidan ya kunyata PDP yayin da ya gaza tsayuwa kan ikirarinsa na farko cewa shi wakilin jam'iyyar ne a rumfar zaɓe lokacin zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Sunayen Gwamnonin APC, PDP Da A Halin Yanzu Ke Kokarin Kwaton Kansu A Kotu Kan Matsalar Takardun Karatu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262