Jirgin Shugaban Kasa Tinubu Zai Lula Kasar Kenya Don Halartan Taron AU
- Jirgin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa babban birnin Nairobi da ke kasar Kenya don halartan taron AU wanda za a yi a ranar Lahadi
- Ana sa ran Tinubu zai gabatar da rahoton harkokin ECOWAS a gaban sauran shugabannin kasashen Afrika
- Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake ya bayyana, Tinubu zai dawo da zaran an kammala taron
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Nairobi, kasar Kenya, a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli domin halartan taron tsakiyar shekara na gamayyar kungiyoyin hadin kan Afrika.
Kakakin shugaban kasar, Dele Alake, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 15 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya ce a matsayinsa na shugaban ECOWAS, Tinubu zai bi sahun sauran shugabannin kasashe da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka da sauran manyan masu fada aji zuwa wajen taron da za a yi a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli.
Shugaban kasa Tinubu zai gabatar da rahoto a taron
Ya kuma ce shugaban kasa Tinubu zai gabatar da wani rahoto kan irin ci gaban da kungiyar ta samu cikin watanni shida da suka gabata a bangaren kasuwanci, walwala, zuba jari, samar da ababen more rayuwa, zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Taron zai hada shugabanni daga Comoros, Botswana, Burundi, da Senegal da kuma shugabannin sauran rassan kungiyoyin tattalin arziki takwas.
A cewarsa, wadannan kungiyoyi na tattalin arziki sun hada ECOWAS karkashin jagorancin Najeriya, kungiyar kasashen gabashin Afirka (ECA), kungiyar ci gaban gwamnatocin kasa da kasa (IGAD), Kungiyar kasuwancin bai daya ta kasashen gabashi da Kudancin Afirka (COMESA).
Sauran sune kungiyar kasashen kudancin Afirka ta (SADC), kungiyar kasashen yankin Sahel (CEN SAD, Kungiyar kasashen yankin Magreb (UMA), da kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta tsakiya (ECCAS), sashin Hausa na BBC ya rahoto.
Ban taba sanin zan zama shugaban kasa ba, Tinubu ga tsoffin gwamnonin 1999
A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai taba sanin cewa zai dare kan kujera ta daya a kasar ba.
A cewar kakakin shugaban kasar, Dele Alake, Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga rukunin gwamnonin 1999 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng