Masu Garkuwa Da Mutane Sun Dauke Likita Bayan Yin Basaja a Matsayin Marasa Lafiya a Calabar
- Wasu da ake kyautatan zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace wata likita a jihar Kuros Riba
- Mutanen da aka ce sun ɓatar da kama matsayin marasa lafiya, sun yi nasarar ɗauke likitar mai suna Ekanem Ephraim
- Sai dai rundunar 'yan sandan jihar, ta bayyana cewa tuni jami'anta suk bi sahun 'yan bindigar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Calabar, Cross River - A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wata likitar asibitin koyarwa na jami’ar Calabar (UCTH), Farfesa Ekanem Ephraim daga gidanta.
Shugaban ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kuros Riba, Dakta Felix Archibong, ne ya bayyana haka ranar Juma'a a Calabar babban birnin jihar kamar yadda PM News ta wallafa.
Mutanen sun yi basaja a matsayin marasa lafiya
Felix ya bayyana cewa mutanen sun je gidan likitar ne a matsayin marasa lafiya, inda suna cikin magana ne suka ciro bindiga, sannan suka yi gaba da ita.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ƙara da cewa sun sami tabbacin cewa masu garkuwa da mutane ne saboda har sun tuntuɓi 'yan uwanta suna neman kuɗin fansa.
Felix ya kuma yi kira ga gwamnan jihar ta Kuros Riba da ya yi ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kuɓutar da likitar.
Yan sanda sun bi sawun mutanen da suka ɗauke likitar
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar ta Kuros Riba, DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ugbo ta ce tuni jami’an rundunar 'yan sandan jihar suka fara bin sahun masu garkuwa da mutanen domin gano ina suka kai likitar da suka sace gami da kuɓutar da ita.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya ce a baya-bayan nan masu garkuwa sun sha farmakar ma'aikatan lafiya a jihar, lamarin da ya sa NMA gudanar da yajin aiki don ganin an amso mutanen nasu.
Masu garkuwa da mutane sun halaka matashin ɗan kasuwa a Bauchi
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wani matashin ɗan kasuwa da masu garkuwa da mutane suka kashe a jihar Bauchi.
An bayyana cewa masu garkuwar sun buɗe wuta ne bayan da yunƙurin shiga gidan matashin ya ci tura.
Asali: Legit.ng