EFCC Ta Kama 'Yan China 13 Saboda Hakar Ma'adinai Ba Bisa Ka'ida Ba a Jihar Kwara
- Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), ta kama wasu 'yan ƙasar China 13 a jihar Kwara
- Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutanen ne bisa laifin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba
- EFCC ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama ba sa da takardar izinin yin aiki a Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ilorin, Kwara - Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta ce ta kama wasu 'yan ƙasar China 13 saboda haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kwara.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwijaren ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a shafin EFCC na Tuwita.
Hukumar ta ce an kama mutanen da suka ƙunshi maza 12 da mace ɗaya a yankin GRA da ke Illorin babban birnin jihar Kwara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kama su saboda haƙar ma'adinai ba tare da izini ba
Hukumar ta EFCC ta ce bayanan da ta samu kan ayyukan da mutanen ke aikatawa ta ƙarƙashin ƙasa da kuma rashin biyan kuɗaɗen haraji ga Gwamnatin Tarayya.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, laifin da suka aikata ya saɓa da sashe na 1(8) (b) na kundin laifuka na 1983.
A yayin da aka tuhumesu, sun amsa cewa suna aiki ne ga wani kamfani mai suna W. Mining Global Services Limited, da ke a Olayinka a ƙaramar hukumar Ifelodun da ke jihar ta Kwara.
Wasu daga cikin ma'aikatan ba su da izinin aiki a Najeriya
EFCC ta ƙara da cewa kamfanin na sarrafa sinadarin giranayit ne domin samar da tayils da suke siyarwa a kasuwannin cikin gida.
A yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa wasu daga cikin ma'aikatan 'yar ƙasar China da aka kama ba sa da takardar izinin yin aiki a Najeriya.
Hukumar ta ce za a gurfanar da su a gaban ƙuliya da zarar an kammala bincike.
Tsohon sanata ya garzaya kotu don hana EFCC bincikarsa
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa tsohon sanatan Bauchi ta Arewa, Muhammed Adamu Bulkachuwa, ya je kotu don neman hana EFCC da sauran hukumomi kama shi.
An bayyana cewa sanatan ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta hana hukumomi bincikarsa kan kalaman da ya yi a lokacin da yake majalisa.
Asali: Legit.ng