Matashi Mai Bukata Ta Musamman Ya Fashe Da Kuka a Bidiyo Bayan Matarsa Ta Gwangwaje Shi Da Kyautar Mota
- Wani mai bukata ta musamman ya fashe da kuka bayan matarsa ta yi kyautar bazata a ranar zagayowar ran haihuwarsa
- Matar wacce ta kasance farar fata ta samu wani kamfani da ke yi wa mutane bazata don kaiwa mutumin kyaututtukan da suka hada da hadaddiyar mota
- Mijin nata ya zauna a kasa sannan ya fashe da kuka yayin da yake dudduba kyaututtukan harma ya ce mata ta karbi motarta wacce itace ta uku da take ba shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mai bukata ta a jihar Imo ya fashe da kuka yayin da matarsa ta yi masa bazata da sabuwar mota da sauran kyaututtuka a ranar zagayowar haihuwarsa.
Mutumin ya yi magana da matarsa, Dinora Okonkowo ta bidiyo yayin da ya yaba kokarinta duk da cewar bata a kasar.
Inyamurin ya yi mamakin dalilin da yasa matarsa wacce baturiya ce take tsananin sonsa duk da kasancewarsa gurgu mai kafa daya sannan ya mato a kanta.
Rikici Yayin Da Mai Kara Ya Fashe Da Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Ke Kara Alfarma, Ya Fadawa Kotu Dalilansa
"Wanene ni da matata take sona haka, mutum Mai kafa daya, mutum mai kafa daya kawai, o Allah tana bina bashi a rayuwa da duk wani farin ciki na rayuwa @Lolo Agu (Dinora Okonkowo)," ya rubuta yayin da ya yada wani bidiyo da ke nuna lokacin da aka kawo masa kyaututtukan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani kamfani Mai yi wa mutane bazata ne ya gabatarwa mutumin da kyautar da suka hada da lemun alfarma, kek da waya.
Mutumin ya roki matarsa da ta mayar da motar, cewa baya bukatarta domin ita ce ta uku da take kawo masa.
Kalli bidiyon a kasa:
Karamcin Dinora Okonkowo ya tsuma zukata
Munachiso ya ce:
"Abun ya kayatar, abun ya yi dadi da kyau!! Ina sonsa!! Barka da zagayowar ranar haihuwarka!!"
user3919164860887 ya ce:
"Ka murmusa, ka cancanci fiye da haka, kana da kyau da dattako sannan Allah ya baka mace mai sonka da kulawa."
Nwachinemere176 ya ce:
"Allah ya yi maki albarka Misis Agu. Barka da zagayowar ranar haihuwarka dan uwa Allah ya karo shekaru masu albarka da sunan Yesu, Amin."
Queen mercy6052 ta ce:
"Na tayaka murna wannan shine soyayya ta gaskiya ba maganar kafa bace maganar yadda kake Sa ta ji ita ta daban ce."
Budurwa a shiga tsaka mai wuya yayin da saurayinta ya aike mata 500K bayan ta kama shi yana cin amanarta
A wani labari na daban, mun ji cewa wata budurwa yar Najeriya mai suna Precious ta shiga cikin rudani bayan saurayinta ya aike mata da rabin miliyan saboda ta kama shi yana cin amanarta.
Precious ta bayyana a Twitter cewa ta kai masa ziyarar bazata sakamakon dawowa da ya yi daga tafiya sannan ta shiga gidan nasa da sifiyar makuli.
Asali: Legit.ng