MURIC Ta Soki Gwamnan Lagos Kan Tauye Wa Musulmai Hakkin Yin Addini, Ta Nemi A Yi Gyara

MURIC Ta Soki Gwamnan Lagos Kan Tauye Wa Musulmai Hakkin Yin Addini, Ta Nemi A Yi Gyara

  • Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da saka jarabawar dalibai dai-dai lokacin sallar Juma'a a jihar Lagos
  • Kungiyar ta tura sakon gaggawa ga ma'aikatar ilimi da kuma gwamnan jihar Lagos, Sanwo-Olu don yin gyara
  • Kungiyar ta ce wannan ya sabawa hakkin gudanar da addini na malamai da kuma daliban da abin ya shafa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Lagos - Hukumar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta ja hankalin gwamnatin jihar Lagos kan yadda aka tsara jadawalin jarabawar zango na uku a jihar.

Daliban makarantun gwamnati sun fara jarrabawar zango na uku a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli.

MURIC Ta Soki Gwamnan Lagos Kan Tauye Wa Musulmai Hakkin Yin Addini
MURIC Ta Ce Wannan Mataki An Yi Shi Ne Don Musgunawa Musulmin Jihar Lagos. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Yayin da jadawalin ya nuna za a yi jarabawa a gobe Juma'a 14 ga watan Yuli dai-dai lokacin sallar Juma'a.

MURIC ta yi martani kan tauye wa Musulmai hakki

Yayin mai da martani, shugaban MURIC, Dakta Busari Jamiu-Ademola ya ce hakan tauye hakkin malamai ne da dalibai na 'yancin yin addininsu.

Kara karanta wannan

An Yi Jana’izar Surukin Sarkin Musulmi Da Sarkin Bichi a Kano, An Sada Shi Da Gidansa Na Gaskiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin sanarwar, Busari ya ce:

"Abin takaici ne yadda jadawalin jarrabawar zango na uku a wannar shekara a makarantun jihar Lagos bai yi duba ga 'yancin addini na Musulmai ba.
"Daruruwan malamai da dalibai Musulmai za a hana su samun damar gabatar da sallar Juma'a a ranar 14 ga watan Yuli."

Ta roki gwamnatin Lagos don yin gyara a lamarin

Sanarwar ta kara da cewa:

"Ta tabbata jarabawa ta uku a ranar za a yi ta ne da misalin karfe 1:45 na rana, yayin da jarabawa ta biyu za ta kare da misalin karfe 1:00 na rana.
"Wannan take hakkin mutane ne, ta yaya Musulmai malamai da dalibai za su gudanar da sallar Juma'a a wannan rana?"

Dakta Busari ya roki ma'aikatar ilimi a jihar da kuma Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya ba da umarnin gyara wannan jadawali don ba wa Musulmai damar yin salla.

Kara karanta wannan

Da Gaske Wike ‘Karamin Mahaukaci Ne’? Hadimin Atiku Ya Yi Martani Ga Furucin Fayose

Ya kara da cewa sanin kowa ne a jihar Lagos ana fara sallar Juma'a ne daga karfe 1:00 zuwa 2:30 da rana, Daily Nigerian ta tattaro.

MURIC Ta Zargi Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Da Yi Wa CAN Aiki

A wani labarin, Kungiyar MURIC ta soki gwamnan jihar Osun, Ademola Adelele kan sunayen kwamishinonin jihar.

A makon da ya gabata ne Gwamna Adeleke ya tura sunayen kwamishinonin zuwa majalisar jihar.

MURIC ta ce ana nuna wariya ganin yadda Musulmai bakwai ne kadai yayin Kiristoci sun kai sha bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.