Rai Bakon Duniya: An Yi Jana’izar Surukin Sarkin Musulmi Da Sarkin Bichi a Kano
- Dandazon jama'a da manyan masu fada aji sun halarci jana'izar Malam Imam Galadanci a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli
- An yi jana'izar Galadanci wanda ya kasance surukin Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi a jihar Kano bayan an dauko gawarsa daga birnin Landan
- Babban limamin masallacin kasa da ke Abuja ne ya sallaci gawarsa a fadar mai martaba Sarkin Kano
Jihar Kano - An yi jana'izar Malam Imam Galadanci, surukin Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gawar Galadanci ya isa Kano daga birnin Landan a ranar Talata, 11 ga watan Yuli.
Babban limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Shehu Ahmad ne ya jagoranci sallatar gawar marigayi Galadanci a fadar mai martaba sarkin Kano, inda manyan masu fada aji suka hallara.
Babban bango ya fadi, jama'a sun fadi kyawawan halayyan marigayi Galadanci
Da yake magana jim kadan bayan sallare, Dr Gwani Farouk ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ya yi rayuwa mai inganci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Abun ya yi mani ciwo sosai saboda shi ne ya dauke ni aiki don koyar da harshen Hausa a makaranta. Mutane da dama da kuka gani a nan duk dalibansa ne.
"Ya kasance mutum mai tsananin gaskiya, hakuri, mai himma sosai kuma yana da kyakkyawar alaka da kusan dukkanin malamai. Ya kasance madubin dubanmu kuma ya anyi babban rashi ba wai a Kano kawai ba harma a Najeriya baki daya."
Hakazalika da yake jawabi, tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idris ya ce:
"Wannan babban rashi ne ba wai ga mu yan Kano ba kawai harma ga kasar baki daya. Mun rasa uba, malami kuma madubin duba ga dukkanmu saboda ya yi rayuwa mai matukar muhimmanci wanda ya cancanci kowa ya yi koyi da shi.
"Ya zama dole mu yi alhinin wannan babban rashi. Za mu yi kewarsa saboda hikima da tawali’u da yake koyarwa kuma duk mun koyi da haka”.
Manyan mutane da suka halarci jana'izarsa sun hada da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, da sauransu.
Surukin Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi ya rasu a Landan
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi na jihar Kano, Alhaji Nasir Ado Bayero, sun yi rashin dan uwansu Abubakar Imam Galadanchi.
Marigayin ya rasu ne a birnin Landan bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda majiya ta bayyana.
Asali: Legit.ng