Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Wahala, Tinubu

Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Wahala, Tinubu

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ya fahimci irin wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur
  • Tinubu ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri domin duk abun da ake yi saboda amfanin kasar da ci gabanta ne
  • Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa yana nan zuwa da kayan tallafi don rage radadin da mutane ke ciki

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya fahimci mawuyacin halin da cire tallafin man fetur ya jefa yan Najeriya a ciki, yana mai ba da tabbacin cewa saboda ci gaban kasar ne, musamman saboda makomar kasar a gaba.

Tinubu wanda ya karbi bakuncin tsoffin gwamnoni 18 da suka yi aiki tare da shi a 1999, a fadar shugaban kasa, ya roki yan Najeriya da su kara hakuri, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fada Wa Gwamnonin 1999 Wasu Kalamai Masu Jan Hankali a Aso Villa

Shugaban kasa Bola Tinubu
Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Wahala, Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Kayan rage radadi na gab da zuwa, Inji shugaban kasa Tinubu

Ya ba yan Najeriya tabbacin cewa ana nan ana kokarin aiwatar da tsarin da zai rage radadin illar da cire tallafin man fetur din ya yi, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa manufar zai amfani yan Najeriya da dama maimakon wasu yan tsiraru.

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kara kokari sannan ta hanzarta wajen aiwatar da shirin tare da tabbatar da ingantaccen tsari wanda ba za a yi kutse a cikinsa ba, musamman wajen tura kudi.

Ya ce:

"Na fahimci cewa mutanenmu na shan wahala amma babu yadda za a haifi da ba tare da jin zafi ba.
Dadin haihuwa shine saukin da ke zuwa bayan radadin. An riga an sake haifo Najeriya da cire tallafin mai . An sake haifo kasar don mutane da yawa su amfana maimakon yan tsiraru. Don Allah ku fada wa mutane su dan kara hakuri.

Kara karanta wannan

Wasu Darusa 4 Da Aka Fahimta Daga Nasarar Tinubu Da Shettima a Zaben 2023, El-Rufai

"Kayan rage radadi na nan tafe. Bana son shirin tura kudi ya fada a mugayen hannu. Na san abun na suka kuma yana da matukar wahala. A karshe, za mu yi murna da ci gaban da kasarmu za ta samu."

Tinubu ya nemi amincewar majalisa don ciyo bashin N500bn domin ragewa yan Najeriya radadi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar wakilai wasika, yana neman a yi garambawul kan kasafin kudi na shekarar 2022 domin ba shi damar ciyo bashin naira biliyan 500 don samar da kayyaki na tallafi ga ‘yan Najeriya.

Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar shugaban a zaman majalisar na ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng