Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Sa Labule Da Gwamnan Zamfara Dauda Lawal

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Sa Labule Da Gwamnan Zamfara Dauda Lawal

  • Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS), Manjo Janar Christopher Musa, na gana wa yanzu haka da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal
  • Duk da babu wani bayani kan maƙasudin taron amma ana hasashen ba zai rasa alaƙa da matsalar tsaron da ta addabi Zamfara ba
  • A kwanan nan, wasu 'yan ta'adda suka kashe 'yan sanda huɗu a shingen binciken ababen hawa a Zamfara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Manjo Janar Christopher Musa na gana wa yanzu haka da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal a hedkwatar tsaro da ke Abuja.

Duk da ba bu cikakken bayani dangane da maƙasudin wannan zama har zuwa yanzu da muka haɗa muku rahoto, ana ganin taron zai maida hankali kacokan kan kalubalen tsaron da ya addabi Zamfara.

Babban hafsan tsaro da gwamna Lawal na Zamfara.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Sa Labule Da Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Hoto: Christopher Musa, Governor Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna Lawal ya isa babbar hedkwatar tsaron rundunar soji da misalin ƙarfe 12:22 na rana yau Laraba tare da rakiyar wasu hadimansa.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Nada Tsohon Hadiminsa Mukami Mai Muhimmanci

Haka zalika an ga lokacin da babban hafsan tsaro na ƙasa tare da manyan jami'an soji suka shiga ɗakin taro da gwamnan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene asalin dalilin wannan gana wa?

Wani jami'i, wanda baya son a ambaci sunansa, ya shaida wa jaridar cewa a yanzu an zura wa rundunar sojin Najeriya ido domin ganin yadda zata magance lamarin 'yan bindiga a Zamfara.

A cewarsa, wannan ne babban batun da ya sa babban hafsan tsaro da gwamna Lawal suka sa labule yau Laraba, 12 ga watan Yuli, a birnin tarayya Abuja.

"Bayan taya juna murna, zasu tattauna da lalubo dabarun magance matsalar tsaron da ta addabi jihar gwamna Lawal da sauran jihohin ƙasar nan," inji shi.

Arewa maso Yamma na fama da hare-haren ta'addanci da kashe-kashe, kuma na baya bayan nan da ya faru shi ne wanda yan bindiga suka kashe jami'an yan sanda a Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamna Sani Ya Fara Shirin Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Kaduna, Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaro 3

Gwamna Sani Ya Fara Yunkurin Dawo da Zaman Lafiya, Ya Gana da Hafsoshin Tsaro 3

A ɗazu kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya gana da manyan hafsoshin tsaro 3 a shirinsa na haɗa hannu da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a Kaduna.

Malam Uba Sani ya gana da CDS, shugaban rundunar sojin ƙasa da shugaban rundunar sojin samn Najeeiya kuma ya bayyana abinda suka tattauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262