"Yana Sa Jiki Na Kyarma": Shugaban ABU Ya Bayyana Abin Da Wasu Lakcarori Suka Fada Kan Magudin Zabe
- Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Farfesa Kabiru Bala ya bayyana yadda yake ji in ana labarin magudin zabe
- Ya ce yakan ji jikinsa na rawa idan wani malamin jami’a ya yi tutiyar aikata magudi a zabukan da suka gabata
- Ya kuma ce duk da hakan, akwai bukatar shigo da karin malaman jami’o’in kasar nan cikin hidimar zabe don inganta ta
Zaria, Kaduna - Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, Farfesa Kabiru Bala, ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu malaman jami’o’in da ke gudanar da ayyukan zabe a kasar na.
Ya ce duk da wasu bara gurbi da ake samu a cikin malaman jami’o’in, akwai bukatar a kara yawan malam cikin harkokin don samun dorewar ingantaccen zabe a Najeriya kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Farfesa Bala ya bayyana hakan ne wajen taron da sashen nazarin kimiyyar siyasa da harkokin kasa da kasa na ABU, tare da hadin gwiwar gidan Mambayya na Jami’ar Bayero Kano suka shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Bala ya ce malaman jami’o’in Najeriya za su iya kawo sauyi a harkar zabe
Farfesa Bala ya ce malaman jami’a wasu rukuni ne na mutane da za a iya aminta da su saboda gaskiyarsu da rikon amanarsu.
Ya kara da cewa idan ana son samun ingattacen zabe, sai a yi kokarin yi wa tsarin gudanar da zaben garambawul.
Bala ya kuma ce idan malaman jami’an ne ake tunanin za su iya kawo gyara a tsarin zaben da kansu, to sai a yi kokarin basu cikakkiyar dama kan hakan.
Baya jin dadi idan wani malamin jami’a ya yi ikirarin aikata magudin zabe
Farfesan ya kara da cewa akwai ra’ayoyi mabanbanta dangane da yadda wasu daga cikin malaman jami’o’in suka gudanar da ayyukansu a lokacin babban zaben da ya gabata.
Kabir Bala ya ce yakan ji jikinsa ya kama rawa a duk lokacin da wasu daga malaman jami’o’in suka yi ikirarin taimakawa wani dan siyasa wajen aikata magudin zabe.
Ya ce shi ya san abinda aikata a lokacin da yake gabatar da aikinsa a zaben da ya gabata.
An bayyana yawan ministocin da Tinubu zai nada a gwamnatinsa
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, da ya bayyana yawan ministocin da Shugaba Tinubu zai nada.
Ya ce Tinubu na da ikon nada daga ministoci 36 har zuwa guda 42 duba da cewa kundin tsarin mulki ya tilastawa shugaban kasa nada ministoci daga kowace jiha.
Asali: Legit.ng