An Ayyana Aliko Dangote Wanda Ya Fi Kowa Kudi a Afrika a Karo Na 12 a Jere
- An bayyana cewa har yanzu Aliko Dangote ne ke riƙe da matsayin mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afrika
- Dangote shi ne ɗan Najeriya ɗaya tilo da ga shiga jerin masu kuɗi 200 na duniya na mujallar Forbes
- Haka zalika kamfanin simintin Dangote ne mafi girma da samar da siminti a Afrika
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanoni na Dangote, ya sake zama wanda ya fi kowa kudi a Afrika kamar yadda shafin ƙididdigar masu kuɗi Forbes ya wallafa.
Dangote dai ya ci gaba da zama na ɗaya a kuɗi a Afrika duk da irin faɗi tashin da ake samu a harkokin kasuwanci a cikin shekarun baya-bayan nan.
Dangote da wani attajiri ɗaya kaɗai ne suka shiga jerin masu kuɗin duniya daga Afrika
Dangote, wanda ya shahara a ɓangaren samar da siminti, shi kaɗai ne ɗan Najeriya da ya shiga jerin manyan masu kuɗin duniya 200.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An bayyana cewa Aliko Dangote da babban attajirin nan Johann Rupert ɗan ƙasar Afrika ta Kudu ne kaɗai suka shiga jerin masu kuɗin a nahiyar Afrika.
An bayyana cewa a yanzu haka Dangote na da tarin dukiya da aka ƙiyastata yawanta a dala biliyan 14.2 wacce ta ƙaru daga dala biliyan 12.1 da take a shekarar da ta gabata.
Shafin na Forbes ya bayyana cewa karyewar hannayen jari da samun ƙaruwar kuɗaɗen ruwa na daga cikin abubuwan da suka yi ƙasa da masu kuɗi da yawa a shekarar 2023.
Kamfanin siminti Dangote ne mafi girma a Afrika
An bayyana kamfanin na Dangote a matsayin wanda ya fi kowane samar da siminti a nahiyar Afrika, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Kamfanin wanda yake da resuka 10 a ƙasashe daban-daban na Afrika, yana samar da aƙalla tan miliyan 51.6 a duk shekara.
A kwanakin baya ne attajirin ya ƙaddamar da babbar matatar mai a Legas, wacce ake ganin za ta yi gogayya da sauran manyan matatun mai na duniya.
Mai kamfanin BUA ya rabawa makarantu 22 tallafin maƙudan kuɗaɗe
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan attajirin nan ɗan asalin garin Kano, Abdulsamad Isiyaka Rabiu da ya rabawa makarantu 22 tallafin kuɗaɗe naira biliyan 22.
A ƙarƙashin tsarin da mai kamfanin BUA ya fitar, kowace makaranta za ta samu abinda ya kai naira miliyan 250.
Asali: Legit.ng