Majalisa Ta Dakatar Da Karin Kudin Karatun Jami'a Da Aka Yi
- Majalisar wakilai ta buƙaci jami'o'in gwamnatin tarayya ɗa su dakatar da aiwatar da shirin ƙarin kuɗin makaranta
- Majalisar ta yi nuni da cewa ƙarin kuɗin karatun zai kawo koma baya inda ɗalibai da dama za su haƙura da karatu
- Ta umarci gwamnatin tarayya da ta ƙara kasafin kuɗin da ta ke warewa ɓangaren ilmi a ƙasar nan domin inganta shi
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta buƙaci jami'o'i da su dakatar da aiwatar da sabon tsarin ƙarin kuɗin makaranta wanda tace zai sanya ɗalibai da dama su haƙura da karatu.
Majilisar wakilan ta kuma buƙaci ma'aikatar ilmi ta ƙasa da ta gaggauta duba kan sabon tsarin biyan kuɗin a kwalejin gwamnatin tarayya a koma wanda ake amfani da shi a baya, cewar rahoton The Nation.
Jaridar Channels tv tace majalisar ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan ƙara yawan kuɗin da ta ke kashewa a ɓangaren ilmi domin tabbatar da cewa ɗalibai sun samu ingantaccen ilmin firamare da na sakandire.
Majalisar za ta binciki ƙarin kuɗin karatun da aka yi
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka kuma majalisar ta amince za ta binciki ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'on gwamnatin tarayya suka yi da ƙarin kuɗin makaranta a kwalejojin gwamnatin tarayya a ƙasar nan, domin samun mafita mai kyau kan ƙalubalen da ɓangaren ilmin ke fuskanta.
Majalisar ta cimma hakan ne bayan ƙudirin Hon. Aliyu Sani Madaki kan buƙatar dakatar da aiwatar da ƙarin kudin makarantar jami'o'in gwamnatin tarayya, da ƙudirin Saidu Musa Abdullahi da Hon. Kama Nkemkanma kan dakatar da ƙarin kuɗin makarantun sakandire na 'Unity Schools'.
Madaki ya ce saboda ƙarancin isassun kuɗi domin ilmin gaba da sakandire da hauhawar farashi, jami'o'in gwamnatin tarayya sun ƙara kuɗin karatu daga kaso 100% zuwa kaso 200% yayin da aka ƙara kuɗin ɗakin kwanan ɗalibai daga 50% zuwa 100%.
Wata Kungiya Ta Ankarar Da Hukumomi Kan Shirin Ganduje Na Sulalewa Daga Kasar Nan, Ta Bada Shawarar Abun Da Za Ayi Masa
Gwamnan Taraba Ya Rage Kudin Karatun Jami'a
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Taraba ya zaftare kuɗin karatu a jami'ar jihar da kaso 50%.
Gwamna Agbu Kefas ya ɗauki wannan matakin ne domin rage raɗaɗin halin matsin da ake ciki a dalilin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng