Gwamna Zulum Ya Haramta Sana'ar Jari Bola a Daukacin Jihar Borno

Gwamna Zulum Ya Haramta Sana'ar Jari Bola a Daukacin Jihar Borno

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya haramta sana'ar jari-bola a faɗin jihar baki ɗaya
  • Ya bayyana hakan ne bayan cin karo da tarin kayan gwamnati da ya yi a wani waje na sana'ar jari-bola
  • Gwamnan ya ce sun ɗauki matakin ne don kare masu sana'ar daga hare-haren 'yan Boko Haram

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Maiduguri, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da haramta sana'ar jari-bola a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 27.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi ranar Litinin, a Maiduguri babban birnin jihar Borno, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Zulum ya hana sana'ar bola-bola a jihar Borno
Gwamna Zulum ya haramta sana'ar jari-bola a kananan hukumomi 27 na jihar Borno. Hoto: @bldr_kashim
Asali: Twitter

Dalilin Gwamna Zulum na hana sana'ar jari-bola

Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki wannan mataki ne domin kare masu sana'ar daga kisan da 'yan ta'addan Boko Haram ke yi musu a wurare daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan

Hare-Haren 'Yan Bindiga: Dan Majalisar Tarayya Ya Buƙaci Mutanen Jiharsa Su Kare Kansu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma Zulum ya ce an ɗauki matakin domin daƙile sace-sacen wasu kayayyaki na gwamnati da ake tunanin wasu daga cikin masu sana'ar ta jari-bola na yi.

A kalamansa:

“A cikin shekaru biyar da suka gabata, an kashe mutane da dama sakamakon harkar bola-bola. Hakan ya sa gwamnatin jihar Borno gudanar da bincike dangane da sana'ar.”
“Kun ga wannan wurin, duk kadarorin gwamnati ne kuma a bayanku akwai kadarorin kamfanonin sadarwa.”
“Irin waɗannan ayyukan sai dai a kirasu da zagon ƙasa ga tattalin arziƙin Gwamnatin Tarayya da na jihohi.”
“Don haka na ba da umarnin hana jari-bola a dukkanin ƙananan hukumomi 27 har zuwa abinda ya sawwaƙa.”

Gwamnatin jihar Borno ta yi asarar kadarorin na biliyoyin naira saboda 'yan jari-bola

Gwamnan ya ƙara da cewa an san 'yan jari-bola da ɓata kadarorin gwamnati da na sauran al'umma a yankunan da rikicin Boko Haram yai ƙamari.

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata da Dukkan Hadiman Da Magabacinsa Ya Naɗa Nan Take

Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin jihar ta yi asara ta biliyoyin naira daga ayyukan masu sana'ar ta jari-bola kamar yadda aka wallafa a shafin Tuwita na NTA.

Zulum ya ƙara da cewa dokar ta shafi har masu sana'ar siyan manyan ƙarahuna, da masu sassara ƙarahuna gami da jigilarsu a faɗin jihar.

Gwamna Zulum ya yi wa manoman Maiduguri babban gata

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya samar da motocin da za su riƙa jigilar manoman ƙaramar hukumar Damboa zuwa gonakinsu.

Zulum ya ɗauki wannan mataki ne bayan wasu jerin hare-hare da 'yan Boko Haram suka kai a ƙaramar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng