“Karbi N5m”: Wani Mutum Ya Kalubalanci Mai Aikin Ginin Da Ya Sha Alwashin Gina Dankararren Gida Da Miliyan 5
- Wani kararren mai gini, Abraham, wanda ya wallafa wani hoto na gidan da zai iya ginawa kan naira miliyan 5 ya samu aikin yin haka
- Wani kwararre kan bayar da tallafin karatu, Oludayo Sokunbi, wanda ke shakku kan cewa zai iya cimma haka da wannan kudin da ya ce, ya ce a shirye yake ya bashi kudin
- Jama'a sun yi cece-kuce yayin da wasu suka ce mutum ba zai iya taba aiwatar da aikin ba da wannan kudin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mai aikin gini, Abraham, ya yi wani rubutu da ya yadu a Twitter sannan ya ce zai iya gina hadadden gida kan naira miliyan 5.
A lokacin da ya yi rubutun a twitter, mutane da dama sun garzaya sashinsa na sharhi da ayoyin tambaya da nuna shakku, musamman yanzu da kayan gini suka yi tsada.
Matashi zai gina gida da miliyan 5
Wadanda suka yarda da mutumin sannan suka ga hakan a matsayin wata dama mai kyau sun aika masa da sako. Kwararre a kan bayar da taffin karatu, Oludayo Sokunbi, ya shiga yarjejeniya da shi a fili domin gwada ko da gaske zai iya gina gida a kan naira miliyan 5.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wani rubutu da ya yi a Twitter, ya ce:
"Zo mu kulla yarjejeniya a Twitter. Zan tura maka miliyan 5 kuma dole ka isar da aikin. Ka yarda?"
Kalli rubutun a kasa:
Jama'a sun yi martani
@tosinraj ya ce:
"Shin zai ba da fili ma son shiga? Lol."
@oviosu ya ce:
"Mutum zai isar "bacewa" da naira miliyan 5 dinka...."
@_Thurba ya ce:
"A matsayina na mai kiyasta abun da za a kashe a gini, ina ganin za a iya cimma haka da 5M da kayan gina kadan, ko babu kayan gida."
Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo
@Mykoladoo ya ce:
"Kawai za ka yi amfani da 100K wajen hada hoton nan da ya baka sannan ka ji dadinka da sauran miliyan 4.9."
@OyakhireTaiye ta ce:
"Ya fara sanya hannu a yajejeniyar faaa, sannan ya kawo rahoton yan sanda cea bai taba damfarar wani ba."
Matashi ya kera motar G-WAagon, ya tuka ta a bidiyo
A wani labarin, wani matashi dan Najeriya ya kera motar G-wagon da kayayyakin da ya tattara daga nan gida Najeriya.
A cewar matashin, ba injin adaidaita sahu ya yi amfani da shi wajen kera motar ba kamar yadda wasu suke zargi.
Asali: Legit.ng