Gwamnan Jihar Ondo Ya Kara Wa'adin Hutun Neman Magani Har Sai Baba Ta Gani, An Bada Dalili

Gwamnan Jihar Ondo Ya Kara Wa'adin Hutun Neman Magani Har Sai Baba Ta Gani, An Bada Dalili

  • Majalisar dokokin jihar Ondo ta sanar da ƙara wa'adin hutun zuwa neman magani na gwamna Rotimi Akeredolu
  • Kakakin majalisar Rt (Hon) Olamide Oladiji, wanda ya bayar da sanarwar ya ce ƙarin wa'adin zai ba Akeredolu damar hutawa bayan ya warke
  • A cikin takardar wacce ya gabatarwa da majalisar, Akeredolu ya ce mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa, zai ci gaba da jan ragamar jihar har sai idan an yi wata sanarwa saɓanin hakan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Akure, jihar Ondo - Gwamna Olurotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ƙara wa'adin hutun wata ɗaya na neman magani da ya ɗauka har sai baba ta gani.

Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Rt (Hon) Olamide Oladiji, a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, ya tabbatar da ƙarin wa'adin ga manema labarai a birnin Akure, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Dakon Sunayen Minustoci, Ɗan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa AapC

Gwamnan Akeredolu ya kara wa'adin hutun zuwa neman magani
Gwamna Akeredolu ya kara wa'adin ne domin ya huta bayan ya warke Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Dalilin ƙara wa'adin neman maganin da Akeredolu ya yi

A cewar Oladiji, ƙarin wa'adin neman magani ya biyo bayan shawarar da likita ya bayar kan ya samu isashshen hutu bayan ya warke daga ciwon da yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta rahoto cewa Oladiji ya bayyana cewa takardar Akeredolu ta neman a ƙara masa wa'adin hutun neman maganin tana kan tanadin sashi na 190 na kunɗin tsarin mulkin ƙasar nan (da aka yi wa garambawul).

Kakakin majalisar ya bayyana cewa Akeredolu a cikin takardar ya ce mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, zai ci gaba da zama a matsayin gwamna har sai idan an fitar da wata sanarwa saɓanin hakan.

Oladiji ya miƙa godiyarsa ga Allah kan samun lafiyar da gwamnan yake yi inda ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa nan ba da daɗewa ba Akeredolu zai dawo kan aikinsa.

Kara karanta wannan

Bata-Gari Sun Kai Farmaki Kan Sakatariyar Jam'iyyar SDP a Jihar Kogi, Sun Barnata Dukiya Mai Tarin Yawa

Jam'iyyar APC Ta Magantu Kan Masu Yada Jita-Jitar Mutuwar Akeredolu

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Pndo ta bayyana cewa za ta sanya ƙafar wando ɗaya da duk masu yaɗa jita-jitar cewa gwamnan jihar ya yi bankwana da duniya.

Jam'iyyar ta bayyana cewa za ta cafke dukkanin masu cewa gwamna Rotimi Akeredolu ya mutu. Gwamnan dai yana ƙasar wajen neman maganin rashin lafiyar da yake fama da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel