ISWAP Ta Haramta Sana'o'i 3 a Karamar Hukuma Guda a Jihar Borno
- Ƙungiyar 'yan ta'adda ta haramta wa manoma, makiyaya da 'yan su shiga yankuna 8 a ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno
- ISWAP ta zargi mutane da zuwa leken asiri suna gaya wa rundunar sojin Najeriya ayyukan 'yan ta'adda a garuruwan
- Wannan na zuwa ne a lokacin da sojin sama suka ƙara matsa kaimi wajen kai samame mafakar 'yan ta'addan ISWAP
Borno - Ƙungiyar 'yan ta'adda ISWAP ta haramtawa manoma, masu kamun kifi da makiyaya gudanar da sana'o'insu a yankunan da take iko da su a ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno.
Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa ƙungiyar ta hana manoma, 'yan su da makiyaya gudanar da ayyukansu a garuruwan yankin Marte.

Source: UGC
Bayanai sun nuna cewa ISWAP ta sha alwashin halaka duk wanda ta gani yana ɗaya daga cikin waɗan nan ayyuka a garuruwa 8 duk a ƙaramar hukumar Marte, inji rahoton Linda Ikeji.

Kara karanta wannan
Ana Tsaka da Dakon Sunayen Minustoci, Ɗan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa AapC
Sunayen yankunan da ISWAP ta gargaɗi mutane su bar wajen
An tattaro cewa ISWAP ta sha alwashin kawar da duk mutumin da ta kama a yankunan Katikime, Bulungahe, Kutukungunla, Chikun Gudu, Tumbumma, Guma Kura, Guma Gana da sabuwar Marte.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ƙungiyar 'yan ta'addan ta ɗauki wannan matakin ne bayan zargin masu zuwa yankunan na yi wa rundunar sojin Najeriya leƙen asiri, suna faɗa musu bayanai kan 'yan ta'addan.
Sojoji sun samu nasarar sheke mayakan ISWAP da dama
ISWAP ta fitar da wannan sanarwa ne bayan luguden wutan jirgin sojin sama ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙanta da yawa a wasu wurare da aka gano suna ɓuya.
Luguden wutan sojin saman ya sheƙe manyan kwamandojin da ISWAP ke ji da su, mayaƙa, haka nan ya lalata tantunan da suke ɓuya, wurin haɗa makamai da ababen hawansu.
Bugu da ƙari, ruwan bama-baman sojin saman Najeriya ya hana 'yan ta'addan sakat da yancin yawo kuma bisa tilas suka fara tattara kayansu suna barin mafakarsu.

Kara karanta wannan
Dakarun Sojoji Sun Yi Galaba Kan 'Yan Ta'adda Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace a Jihar Arewa
Daga cikin wuraren da sojoji suka yi ruwan wutan sun haɗa da Grazah da Wa-Jahode da ke cikin tsaunin Mandara kuma majiyar soji ta ce an kashe 'yan ta'adda sama da 100.
Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima
A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana muhimman abu 2 da suka haifar da 'yan bindigan daji a arewacin Najeriya.
Ahmad Sani Yerima, ya yi ikirarin cewa talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta'addancin 'yan bindigan jeji a Najeriya.
Asali: Legit.ng