Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano Rasuwa
- Al’ummar karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano sun shiga jimami na wani babban rashi da suka yi
- Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Bebeji, Alhaji Sani Kanti Ranka, rasuwa a ranar Juma'a
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika ta’aziyyarsa tare da yi wa marigayin addu’a samun rahmar Ubangiji
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano, Alhaji Sani Kanti Ranka, rasuwa a daren ranar Juma'a, 8 ga watan Yuli.
Marigayi Sani ya rasu ne bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya kuma an binne shi bisa koyarwar addinin Musulunci a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Twitter
Marigayi Sani mutum ne mai son zaman lafiya, Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin mutuwar

Kara karanta wannan
Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa a kan mutuwar shugaban karamar hukumar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mara hayaniya mai son zaman lafiya da tarin sani a harkar siyasa da bautawa mutane.
Ya kuma yi masa addu'an samun Rahamar Allah da aljannah madaukakiya.
Ya rubuta a shafinsa:
"Cike da bakin ciki na samu labarin mutuwar Alhaji Sani Kanti Ranka, shugaban karamar hukumar Bebeji.
"Ya kasance mutum mai son zaman lafiya da tarin sani a siyasa da yi wa mutane hidima.
"Allah madaukakin sarki ya yafe masa kura-kuransa sannan ya saka masa da kyawawan ayyukansa da aljannatul Firdau. - AKY."
Jama'a sun yi wa mamacin addu'a tare da mika ta'aziyyarsu
@yakubwudil ya yi martani:
"Allah ya rahama masa, yasa aljanna makoma."

Kara karanta wannan
Innalillahi: Sarkin Musulmi da wani fitaccen sarki a Arewa sun yi rashin surukinsu
@ABBAMAIADDA ya ce:
"Allah ya jiƙansa da rahama."
@Aliyusanizaki ya ce:
"Allah ya jikansa."
@bin_saless ya ce:
"Allah Ya gafarta masa Yasa ya huta."
@shaba_isah ya rubuta:
"Allahunma agfirlahum war hamhum wa afu anhum. Aameen."
@mijinyawa77 ya ce:
"Allah ya jikansa ya Kwanta makwanci."
Allah ya yi wa Hajiya Halimatu Attah rasuwa
A wani labarin kuma, mun ji cewa matar nan da ta fi kowa tsufa cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 63 da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris din 2022, ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.
Hajiya Halimatu Attah ta rasu a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli da misalin karfe 6:20 na yamma a Kaduna kamar yadda wani danginta ya bayyana.
Asali: Legit.ng