“Al’ada Shine Tushe”: An yi Cece-Kuce Yayin da Gwamna Oyebanji Ya Duka a Gaban Afe Babalola

“Al’ada Shine Tushe”: An yi Cece-Kuce Yayin da Gwamna Oyebanji Ya Duka a Gaban Afe Babalola

  • Wasu sabbin hotunan gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, da suka yadu a soshiyal midiya sun ja hankalin mutane da dama
  • An gano gwamnan na APC kwance a kasa yana gaishe da dattijon kasa kuma babban lauya Afe Babalola
  • Wannan abu da gwamnan ya yi wanda al'ada ce ta Yarbawa ya sa mutane da dama sun jinjina masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Biodun Oyebanji, gwamnan jihar Ekiti, ya ja hankalin yan Najeriya da dama a soshiyal midiya kan wasu hotunansa da suka yadu a soshiyal midiya inda aka gano shi kwance yana gaishe da wani dattijon kasa, Afe Babalola.

Afe Babalola ya kasance dattijo, shahararren lauya, mai tarin ilimi kuma mamallakin jami'ar Afe Babalola da ke Ekitini. A ranar Litinin, 10 ga watan Yuli ne zai yi bikin cikarsa shekaru 60 da zama lauya.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Gwamnan ya duka yana kai da Afe Babalola
“Al’ada Shine Tushe”: An yi Cece-Kuce Yayin da Gwamna Oyebanji Ya Duka a Gaban Afe Babalola Hoto: @AderonkeW
Asali: Twitter

Yan Najeriya sun yaba ma Gwamna Oyebanji kan dukawa da ya yi wajen gaishe da Afe Babalola

An gano Oyebanji, gwamna kuma shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti kwance a cikin hotuna yana gaishe da jigon kasar, wanda shine yanayin gaisuwa a al'adan Yarbawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na wallafar da wata yar jarida, Arabinrin Aderonke, ta yi inda take alfahari da abun da gwamnan ya aikata, domin tofa albarkacin bakunansu.

Da take wallafar tata, Aderonke ta ce:

"Ni yar jihar Ekiti ce, kuma a nan ga gwamnana, mutumin da nake kira da BAO, yana gaishe da Afe Babalola SAN, wani dan Ekiti kuma dattijon kasa, a al'adar Yarbawa, kamar yadda ya kamata. An yi mana tarbiya sannan an horar da mu kan mu dunga gashe da manyanmu cike da mutuntawa. Ina alfahari da kai, Gwamna BAO."

Kara karanta wannan

Ta Bayyana: Tambuwal, Yari, Wammako Da Wasu Tsaffin Gwamoni 11 Da Ke Karbar Fanso Bayan Zama Sanatoci

Yayin da wasu yan Najeriya suka yba ma gwamnan kan girmama al'ada da fito da iya, wasu sun bukaci Oyebanji da sauya irin wannan yunkuri zuwa shugabanci nagari.

Ga martaninsu a kasa:

Wani mai amfani da Twitter @realtopeomotayo, ya jinjinawa gwamnan

"Gwamnan kirki @biodunaoyebanji madubin duba ga al'ummar Ekiti masu tasowa."

Wani dan kasa mai suna @kunzybaba ya ce:

"Ina fatan yana aiki yadda ya kamata a matsayinsa na Gwamna saboda gaisuwa ba shine hali mai kyau ba."

A nasa martanin, @KayKayl14, ya ce:

"Yadda aka ladabtar da mu a Ekiti. Bama taba barin matsayi ya tauye manyan al'adunmu."

Wani mutum mai suna @Blaqgattuso ya ce:

"'Al'ada ita ce tushe."

Matashi dan Najeriya ya kera motar G-Wagon, ya tuka ta a bidiyo

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya wanda ya kera motar G-Wagon ya kai abar hawar tasa gaban wata mai wasan barkwanci (Mama Uka) don ta duba.

An tattaro cewa wasu mutane na ta kokarin kushe fasahar mutumin, cewa ya yi amfani da injin din adaidaita sahu ne a motar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng