“Ina Bukatar Tallafi”: Matashi Ya Kera Motar G-Wagon, Ya Baje Kolinta a Bidiyo

“Ina Bukatar Tallafi”: Matashi Ya Kera Motar G-Wagon, Ya Baje Kolinta a Bidiyo

  • Wani hazikin matashi dan Najeriya ya kera motar G-Wagon bayan ya tattara kayan kera jikin motar a nan gida
  • Mutumin ya baje kolin motar don gwadawa yayin da ya kunna injin dinta don tabbatar da cewar ba injin din adaidaita ya yi amfani da shi ba
  • Yan Najeriya da suka yi martani kan bidiyonsa sun jinjina masa yayin da suka yi masa addu'an samun tallafin da yake bukata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya wanda ya kera motar G-Wagon ya kai abar hawar tasa gaban wata mai wasan barkwanci (Mama Uka) don ta duba.

Mama Uka ta ce mutane da dama na ta kokarin kushe fasahar mutumin, cewa ya yi amfani da injin din adaidaita sahu ne a motar.

Matashin da ya kera motar G-Wagon ya burge mutane da dama
“Ina Bukatar Tallafi”: Matashi Ya Kera Motar G-Wagon, Ya Baje Kolinta a Bidiyo Hoto: @goddaychukwudieze
Asali: TikTok

G-Wagon din matashin ya burge Mama Uka

An bukaci ya kunna injin din motar a cikin wani bidiyo domin fankar motar ta kada ta yadda kowa zai gani. Mutane da dama sun cika da mamakin abun da ya kirkira.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Janareto Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashin (@goddaychukwudieze) ya ce zai iya kera karin abubuwa da dama, cewa abun da yake bukata kawai shine tallafi na kudi daga wajen mutane.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

omodano ya ce:

"Wannan abu ya yi kyau. Don Allah tsawon wani lokaci ya dauke ka kafin ka kera motar nan?"

akuhittmore ya ce:

"Aiki ya yi kyau."

FAMOUS-CHRIS ya ce:

"Abin mamaki."

Chukunaso ya ce:

"Ya yi kyau."

LOLO EDU ya ce:

"Ci gaba da gashi Allah ne karfinka."

Komolafe victor ya ce:

"Aiki ya yi kyau wa ya lura da vw a g wagon."

Gire ta ce:

"Ma shaa Allah, Allah mai kyauta."

Matashi Ya Kera Motar Wasan Tsere, Ya Tuka Ta a Birnin Edo, Mutane Sun Sha Mamaki a Bidiyo

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zubawa Ango Abinci Yayin da Take Kokarin Manna Masa ‘Kiss’ Ya Girgiza Intanet

A wani labari makamancin wannan, Legit.ng ta kawo a baya cewa wani matashi dan Najeriya ya yadu a soshiyal midiya bayan an gano shi yana tuka motar wasan tsere da ya kera da hannunsa a jihar Edo.

Wata matashiya da ke kan hanyar lokacin da matashin ya wuce ta dauki bidiyonsa sannan ta wallafa a TikTok, cewa abun ya bata mamaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng