Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje Jihar Delta Kwanaki Kadan Bayan Na Abuja

Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje Jihar Delta Kwanaki Kadan Bayan Na Abuja

  • Wani gini mai hawa uku da ake kan aikinsa a jihar Delta ya ruguje ranar Jumu'a 7 ga watan Yuli, 2023
  • Rahoto ya nuna cewa ginin na wani Otal ne kuma har yanzun ba bu tabbacin adadin waɗanda rushewar ta shafa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan bene mai hawa biyar ya kife kan mutane a birnin tarayya Abuja, jami'ai sun ciro mutum 9

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Delta State - Wani ginin bene mai hawa uku da ake kan aiki ba'a kammala ba ya ruguje a yankin Okotomi, Okpanam, karamar hukumar Oshimili ta arewa a jihar Delta.

Channels tv ta tattaro cewa ginin wanda aka ce sabon Otal ne ake gina wa ya kife da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Taswirar jihar Delta a Najeriya.
Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje Jihar Delta Kwanaki Kadan Bayan Na Abuja Hoto: channelstv
Asali: UGC

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton babu cikakken bayani kan ko lamarin ya shafi wasu mutane ko akasin haka.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Yadda ake fama da ibtila'in rushewar gine-gine a Najeriya

Legit.ng Hausa ta fahimce cewa wannan ne na baya-bayan nan a cikin gine-ginen da suka rushe a sassan ƙasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Litinin ta farkon makon nan da ya shige, wani gini mai hawa 5 da ake kan aiki ba'a kammala ba ya rushe a Anguwar Lifecamp cikin babban birnin tarayya Abuja.

Jami'an bada agaji wanda suka ƙunshi jami'an hukumar kai ɗaukin gaggawa (NEMA) sun samu nasarar zaƙulo mafi karanci mutum 9 waɗanda ginin ya danne a birnin tarayya.

Haka zalika a ranar 29 ga watan Yuni, 2023, wani gini da ake aikin ginawa ya rushe a ƙaramar hukumar Obio/Akpor da ke cikin jihar Ribas.

Lamarin dai ya taɓa mutane domin rahotanni sun nuna akalla mutane 4 ginin ya jikkata kuma aka kwantar da su a Asibiti don duba lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar 'Yan Sanda Ta Musanta Rade-radin Kashe Jami'inta, Ta Yi Bayani

Bayan rushewar ginin, Gwamnatin jihar Ribas ta lashi takobin hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a janyo rushewar ginin, Naija News ta ruwaito.

Kwamitin Anambra Ya Tabbatar da Laifin Mmesoma Na Kara Makin JAMB

A wani rahoton na daban kuma Kwamitin da gwamnan Anambra ya kafa domin gano gaskiya kan ruɗanin sakamakon jarabawar Ejikeme Joy Mmesoma ya gama aikinsa.

Kwamitin, wanda gwamna Charles Soludo, ya kafa da nufin gano gaskiya, ya ce aihinin makin da ɗalibar ta ci shi ne 249 ba 362 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262