Yan Sanda Sun Halaka Dan Bindiga, Sun Kama 2 a Jihar Katsina

Yan Sanda Sun Halaka Dan Bindiga, Sun Kama 2 a Jihar Katsina

  • Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da suka kai hari kauyuka a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja, jihar Katsina
  • Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Sadiq, ya ce sun fatattaki yan ta'addan yayin da suka shiga rugar fulani 2
  • Ya ce yayin musayar wuta, jami'ai sun halaka ɗan ta'adda ɗaya kuma sun kama biyu, sun kwato shanu 100

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina - Dakarun 'yan sanda sun samu nasarar halaka ɗan ta'adda ɗaya, sun kama wasu guda biyu kana suka kwato shanu sama da 100 da 'yan ta'adda suka sace a garuruwan Katsina.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

Jami'an yan sanda sun ci nasara a Katsina.
Yan Sanda Sun Halaka Dan Bindiga, Sun Kama 2 a Jihar Katsina Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Ya ce jami'an 'yan sanda sun kai wa 'yan ta'addan samame ne bayan samun wasu sahihan bayanan sirri, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Amarya Yar Shekara 21, Maimunatu Ta Caka Wa Angonta Wuka Har Lahira Kan Karamin Abu a Bauchi

ASP Abubakar ya bayyana cewa bayanan sun nuna cewa wasu yan ta'adda sun kai hari rugar fulani a yankin ƙauyukan Unguwar Rogo da Rafin Gora, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin 'yan sandan ya ce:

"Bayan samun wannan bayanai, DPOn yan sanda na ƙaramar hukumar Ɗanja ya jagoranci dakaru suka yi musayar wuta da maharan, inda suka samu nasarar korarsu da kwato shanu 100."
"Yayin tsaftace wurin da aka yi musayar wutan 'yan sanda suka gano gawar ɗan ta'adda ɗaya da suka sheke."

An gano asalin yan ta'adda biyun da 'yan sanda suka kama

ASP Sadiq ya faɗi bayanan yan ta'adda 2 da suka shiga hannu, Ahmadu Abubakar, ɗan shekara 30 wanda aka fi sani da Mai Boza daga ƙauyen Wagini, ƙaramar hukumar Batsari a Katsina.

Sai kuma Abbas Lawai, wanda aka fi sani da Abbas Dogo ɗan kimanin shekara 40 a duniya daga Polo Quaters a cikin garin Katsina, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar 'Yan Sanda Ta Musanta Rade-radin Kashe Jami'inta, Ta Yi Bayani

Kakakin yan sandan ya kuma tabbatar da cewa yan ta'addan biyu sun amsa cewa da su aka kai wannan hari kuma suna karkashin wani hatsabibin ɗan bindiga, Surajo.

Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana muhimman abu 2 da suka haifar da 'yan bindigan daji a arewacin Najeriya.

Ahmad Sani Yerima, ya yi ikirarin cewa talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta'addancin 'yan bindigan jeji a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262