Na Yi Nadamar Goyon Bayan Jam'iyyar APC, Jaruma Oshodi-Oke
- Jarumar fim ɗin Nollywood Ibironke Oko Anthony da aka fi sani da Ronke Oshodi-Oke ta ce APC ta watsa mata ƙasa a fuska
- Ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da shahararren jami'in yaɗa labaran nan Chude Jideonwo
- Ta ce jam'iyyar APC ta gaza a mulkin da ta gudanar cikin shekaru takwas na baya da suka gabata
Fitacciyar jarumar fim ɗin Nollywood, Ibironke Ojo-Anthony, wacce aka fi sani da Ronke Oshodi-Oke, ta bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki, ta gaza a cikin shekaru takwas ɗin da ta yi mulki a baya.
Ta ce ta yi nadamar goyon baya da kuma tallata jam'iyyar da ta yi bayan abinda ya faru a zanga-zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da fitaccen jami’in yaɗa labaran nan Chude Jideonwo.
Dalilin gudanar da zanga-zangar EndSARS
A watan Oktoban 2020, matasan Najeriya musamman mazauna Legas, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rusasshiyar hukumar jami'an 'yan sanda na musamman wato SARS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar sun buƙaci a kawo karshen cin zarafin da 'yan sandan na SARS ke yi musu. Sun kuma yi amfani da damar wajen neman ingantaccen shugabanci daga masu mulki.
Oshodo-Oke ta kuma ƙara da cewa, ta ji takaicin maganar da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi a lokacin zanga-zangar.
Ta ce ba ta ji ɗaɗin kalaman da gwamnan Legas ya yi ba
'Yar wasan kwaikwayon ta ce ba ta ji ɗaɗin kalaman da ya yi na cewa babu wanda aka kashe yayin zanga-zangar ba.
A cewarta:
“Ina son APC. Ni masoyiyar APC ce, jiki da ruhi na. Na yi tunanin cewa APC za ta kai Najeriya zuwa mataki na gaba."
“Dalilin haka ne ma ko a lokacin da muke yin yaƙin neman zaɓe, ban karɓi kuɗi da yawa ba. Ba kuɗi na zo nema ba, ina hangen abinda zai faru a gaba ne."
Ta ƙara da cewa ta yi wa APC uzuri sosai, saboda a tunaninta shekaru takwas, sun yi kaɗan a gyara Najeriya.
Sai dai ta ce a lokacin zanga-zangar EndSARS, ta rasa duk wani ƙwarin gwiwar da take da shi a kan APC kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Dattijuwa ta tsinewa Peter Obi da jam'iyyarsa Labour
Legit.ng a baya ta kawo muku wani labari kan wata dattijuwa da ta tsinewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Peter Obi, da jam'iyyarsa ta Labour.
Tsohuwar mai shekaru 74 ta koka kan yadda jam'iyyar ta manta da ita duk da harbin bindigar da ta sha a lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng