“Na Rasa Matata Da Yara 5”: Wani Tsoho Da Ke Bara Ya Samu Taimako a Bidiyo Mai Tsuma Rai

“Na Rasa Matata Da Yara 5”: Wani Tsoho Da Ke Bara Ya Samu Taimako a Bidiyo Mai Tsuma Rai

  • Emmanuel Adenule ya rasa matarsa a shekarun baya sannan mutuwa mai yankar kauna ta kuma dauke masa yaransa biyar
  • Emmanuel ya ce yara biyu ne suka rage masa a duniya kuma basu da karfin da za su kula da shi
  • Saboda halin da yake ciki, mutumin wanda zuciyarsa ta karaya ya koma yawon bara a titi sannan wani bawan Allah ya kawo masa dauki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani tsoho mai suna Emmanuel Adenule ya ba da labarinsa mai tsuma zuciya na yadda ya rasa matarsa da yaransa biyar.

Emmanuel ya ce ya rasa matarsa a shekarun baya. Sai dai kuma bai bayyana abun da ya kashe ta ba.

Matashi ya tallafawa tsoho
“Na Rasa Matata Da Yara 5”: Wani Tsoho Da Ke Bara Ya Samu Taimako a Bidiyo Mai Tsuma Rai Hoto: @teaserprank
Asali: Instagram

Bayan haka, mutuwa mai yankar kauna ta kuma rabasa da yaransa biyar, inda ya rage masa yara biyu a duniya.

Wani bawan Allah mai suna @teaserprank a Instagram ya gane shi zaune a kan hanya sannan ya yanke shawarar rage masa radadi.

Kara karanta wannan

“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya tambayi dattijon dalilin da yasa ya zauna cikin damuwa, sannan ya sanar da shi damuwarsa. Ya ce yanzu bara yake yi a titi don samun kudin cin abinci kasancewar ba zai takura sauran yaransa biyu ba.

"Matata ta mutu. Yarana 7. 5 sun mutu yanzu saura biyu kuma sune suke kula da yaran 5 da suka mutu. Ba zan iya daura masu matsalana ba," inji Emmanuel.

Sakamakon taba shi da abun ya yi, Teaser ya kawo wasu damin kudi ya ba tsohon wanda ya fashe da kuka.

Mutane sun tofa albarkacin bakunansu

@kohray1 ta ce:

"Abun tausayi. idan za mu iya nemo shi, zan ji dadin taimaka masa da wani abu. nagode."

@big_daddy_steven01 ya rubuta:

"Ba ka san ma'anar abun da ka aikata yanzu ba, Allah ya yi maka albarka dan uwa kan wannan taimako da ka yi masa, 'ya'yanka da jikokinka ba za su san talauci ba."

Kara karanta wannan

“Ya Fi Sauki”: Matashi Ya Sauya Injin Din Motarsa Zuwa Mai Amfani Da Gas, Yana Kashe Kasa Da N2k Wajen Cika Tanki

@captainaurelian ya ce:

"Duk da abubuwan da ya faru da shi bai manta akwai Allah ba, darasi duk tsananin da kake ciki kada ka yanke kauna da Allah."

Amarya ta zubawa ango abinci yayin da take kokarin sumbatarsa

A wani labarin kuma, wata amarya ta yi wa angonta wanka da abinci ana tsaka da shagalin bikinsu.

Amaryar dai ta yi kokarin nuna wayewarta a filin inda ta dare kan cinyar angon nata sannan ta yi kokarin manna masa kiss sai aka yi rashin sa'a abincin hannunta ya bare masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng