Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Naɗi a Gwamnatinsa, Bayanai Sun Fito

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Naɗi a Gwamnatinsa, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Taiwo Oyedele a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare da garabawul ga harkokin haraji
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ya tabbatar da wannan ci gaban a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023
  • Tinubu ya kafa wannan sabon kwamitin ne domin magance kalubalen da suka yi katutu kan tsarin kasafi da kuma karban haraji a Najeriya

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da naɗin Taiwo Oyedele a mukami mai matuƙar muhimmanci.

Bayan kafa kwamitin tsare-tsaren kasafi da garambawul ɗin harokin haraji, shugaba Tinubu ya amince da naɗin Oyedele a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin.

Shugaba Tinubu da Mista Taiwo.
Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Naɗi a Gwamnatinsa, Bayanai Sun Fito Hoto: Dele Alake, Dolusegun
Asali: Facebook

Tinubu ya naɗa Iyedele a matsayin shugaban kwamitin gyara harkokin haraji

Hadimin shugaban kasa na fannin sadarwan zamani da dabaru, D. O Olusegun, ne ya tabbatar da haka a shafinsa na tuwita ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da ƙari, kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake, ya yi karin bayani kan wanda shugaban ƙasan ya naɗa a matsayin shugaban kwamitin.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Alake ya bayyana cewa:

"Mista Oyedele ya taka matsayin ƙaramin Farfesa a jami'ar Babcock University Business School."
"Haka nan ya yi karatu a makarantun London School of Economics & Political Science, Jami'ar Yale da Harvard Kennedy School Executive Education. Lakcara ne a makarantar koyon kasuwanci ta jihar Legas."
"Haka nan shi ne mutumin da ya kafa gidauniyar taimaka wa nahiyar Afrka (impact Africa) kuma shi ne shugaban gudauniyar."

Shugaban ƙasa Tinubu ya amince da naɗin kwamitin ne domin cika alƙawarinsa na yaye duk wani abu da ya durkusad da kasuwanci, ya hana su bunƙasa a Najeriya.

Jerin Sunaye: Gwamnan PDP Ya Naɗa Jiga-Jigan APC 2 da Wasu 23 a Matsayin Kwamishinoni

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

A wani rahoton na daban kuma Bayan dogon lokaci, gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya naɗa sabbin kwamishinoni bayan kusan wata 9 da hawa mulki.

Daga cikin mutane 25 da gwamnan ya naɗa harda tsoffin kwamishinonin tsohon gwamna Rauf Aregbesola, mamban APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262