Gwamnan Taraba Ya Ayyana Ilimin Firamare da Sakandire Kyauta a Jiharsa
- Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya maida ilimin makarantun Firamare da sakandire kyauta ga 'yan jihar
- Ya ce wannan na ɗaya daga cikin alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe, bayan haka zai rage raɗafin cire tallafin man fetur
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamna Kefas ya zabtare kuɗin jami'a da kaso 50, lamarin da ɗalibai suka yi maraba da shi
Taraba state - Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya ya maida karatun makarantar Firamare da Sakandire kyauta a jihar, in ji rahoton Daily Trust.
Gwamna Kefas ya bayyana wannan kyakkyawan labari ga dalibai da iyaye yayin da ya kai ziyara makarantar Firamare da ke Wukari ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.
A cewar mai girma gwamnan, daga zangon karatu mai zuwa, karatu a makarantun Firamare da Sakandire ya koma kyauta a faɗin jihar Taraba.
Gwamna Kefas ya jaddada cewa gwamnati ya kamata a ce ta ɗauke duk wasu kashe-kashen kuɗi a makarantun, bai kamata a bar ɗalibai da wahalar biyan kuɗi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnan ya maida ilimi kyauta a Taraba?
Agbu Kefas ya kara da cewa ya maida ilimin Firamare da Sakandire kyauta ne domin cika alƙawarin da ya ɗaukar wa al'ummar Taraba lokacin yaƙin neman zaɓe.
Ya ce baya ga cika alkawari, ya yi haka ne domim rage wa mutane raɗaɗi da wahalhalun rayuwa waɗanda suka biyo bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Gwamnan ya zabtare kuɗin jami'a da kaso 50
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan ya maida ilimi kyauta kwanaki kaɗan bayan ya zabtare kuɗin jami'a da ɗalibai ke biya da kaso 50 cikin ɗari domin rage radaɗin da ake fama.
Mafi yawan ɗaliban jami'a mallakin gwamnatin jihar Taraba sun yi murna da farin cikin wannan ragi. A cewarsu rage kuɗin zai taimaka wa rayuwarsu, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Daga Karshe, Gwamna Adeleke Ya Nada Kwamishinoni a Jihar Osun
A wani rahoton na daban kuma Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya naɗa kwamishinoni a gwamnatinsa kusan watanni 9 bayan hawan kan madafun iko.
Kamar yadda aka yi tsammani, an ga sunan tsoffin kwamishinoni 2 da suka yi aiki a zamanin mulkin tsohon gwamna, Rauf Aregbesola, babban jigon APC.
Asali: Legit.ng