‘Ya’yan Tsohon Gwamnan Akwa Ibom Sun Maka Kishiyar Mahaifiyarsu Kotu Kan Rigimar Gidansu Na Gado

‘Ya’yan Tsohon Gwamnan Akwa Ibom Sun Maka Kishiyar Mahaifiyarsu Kotu Kan Rigimar Gidansu Na Gado

  • Gidan tsohon gwamnan mulkin soja na Akwa Ibom, Idongesit Nkanga, ya shiga rudani yayin da ‘ya’yansa suka kai karar kishiyar mahaifiyarsu, Mosun kotu
  • ‘Ya’yan matar farko su hudu sun roki kotu da ta janye takardar izinin mallakar gidan da ta bai wa kishiyar mahaifiyarsu
  • Nkanga dai ya auri Mosun ne bayan ya rabuwarsa da matarsa ta farko a kotu, inda yanzu haka ta haifa masa ‘ya’ya mata biyu, yayin da matarsa ta farko ke da ‘ya’ya hudu

Abuja - ‘Ya’yan tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom su hudu sun bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Jabi Abuja, da ta karbo musu gidansu na gado da ke a babban birnin Tarayya.

Yaran da aka ba da sunayensu da Lance Nkanga, Etietop Nkanga, Utibeabasi Nkanga, Ini-Idara Nkanga da mahaifiyarsu Joanna sun bukaci mai shari’a O. A. Musa, ya soke shaidar mallakin gidansu daga hannun kishiyar mahaifiyarsu Mosun Nkanga.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 a Cikin Wata 1

'Ya'yan Idongesit Nkanga sun kai kishiyar mahaifiyarsu kotu
‘Ya’yan tsohon gwamnan Akwa Ibom sun maka kishiyar mahifiyarsu kotu kan rigimar gidan gado. Hoto: The Sun
Asali: UGC

Mosun tsohuwar matar Mista Nkanga ce, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom na mulkin soja, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Idongesit Nkanga wanda tsohon sojan sama ne, ya rasu a watan Disamban shekarar 2020. An bayyana cewa ya rasu ne sanadiyyar cutar Covid-19, kamar yadda rahoton Channels Tv ya bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bar ‘ya’ya shida, biyu mata daga bangaren Mosun, da hudu maza daga bangaren Joanna, tsohuwar matarsa.

Mista Nkanga ya auri Mosun ne a shekarar 2007 bayan rabuwarsa da Joanna a kotu.

Batun rigimar gidan na su na gado

Yaran ta hannun lauyansu, Inibehe Effiong, sun bukaci alkalin da ya amsa bukatarsu ta neman dakatar da Mosun daga fitar da su daga gidan nasu na gado da ke yankin Asokoro Abuja.

Lauyan ya kara da cewa a yanzu haka da yake Magana a gaban kotun, yaran ba sa da inda za su je su kwana tun bayan korar da kishiyar mahaifiyar ta su ta yi musu.

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

Misis Mosun ta musanta zargin da yaran suka yi

Sai dai a na ta bangaren, Misis Mosun, ta hannun lauyanta, Marvin Omorogbe, ta ce babu bukatar dakatar da ita daga korarsu daga gidan kamar yadda kotun ta ba da umarni a baya.

Ta kuma kara da cewa batun cewa ba sa da gidan da za su zauna ba gaskiya ba ne, domin kuwa lokacin da kotun ta bas u umarnin ficewa daga gidan, sun tafi hutu kasar Faransa.

Alkali ya bayyana abinda zai hana Abba Kyari tafiya gida duk da belinsa da aka ba da

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari.

Sai dai mai shari’a Omotosho wanda shi ne alkalin da ya ba da belin, ya bayyana cewa akwai wasu sharudda da dole sai Abba ya cikasu kafin belin nasa ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng