"Kuɗi Su Ne Komai": Matan Wani Mutumi Sun Kai Masa Amaryar da Ya Aura a Bidiyo

"Kuɗi Su Ne Komai": Matan Wani Mutumi Sun Kai Masa Amaryar da Ya Aura a Bidiyo

  • Wani bidiyon nishaɗi ya nuna uwar gida da mata ta biyu sun ɗauki amarya sun kai wa Mijinsu a matsayinta na matarsa ta uku da ya ƙaro
  • An ga mutumin yana murmushi cikin farin ciki yayin da yake dakon matansa biyu da suka riƙo hannuwan amarya su ƙariso inda yake zaune
  • Lokacin da suka isa wurin mijinsu, ba tare da ɓata lokaci ba suka damƙa masa amarya kuma alamu sun nuna ya ji daɗi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyon nishaɗi da aka wallafa a shafin sada zumunta TikTok, ya nuna alamun za'a yi zaman lafiya tsakanin matan wani mutumi da sabuwar amaryar da ya auro a mata ta 3.

Bidiyon ya nuna a wurin shagalin bikin ta uku, uwar gida da mata ta biyu da kansu suka kamo hannun Amaryar mijinsu, wacce zata shigo a mata ta 3, suka kai wa mai gida.

Kara karanta wannan

Karshen Kyau: Budurwa Ta Saki Bidiyon Cauɗa-cauɗan Kawayenta Suna Wani Abu, Ta Bar Maza Baki Buɗe

Mata 2 sun kai wa Mijinsu amaryar da ya auro.
"Kuɗi Su Ne Komai": Matan Wani Mutumi Sun Kai Masa Amaryar da Ya Aura a Bidiyo Hoto: @cpuntryghana
Asali: TikTok

An ga magidancin tsaye yana jiran su kawo masa sabuwar amaryarsa cikin ƙosawa, uwar gida da mata ta biyun duk sun sanya kaya iri.

Matan guda biyu sun riko hannun sabuwar abokiyar zamansu suna tafiya cikin kwarin guiwa amma alamu sun nuna ita Amarya tana jin kunya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwar gida da mata ta 2 sun kai wa mijinsu amarya

Lokacin da suka ƙarisa inda mijin ke tsaye, matan biyu sun damƙa masa matar da ya auro ta uku cikin fara'a da murmushi. Sun nuna amince wa da auren mijin kuma sun shirya zama tare.

Bidiyon yadda ta wakana tsakanin mata 2 da amaryar mijinsu

Wasu daga cikin ra'ayoyin waɗanda suka kalli bidiyon

@ArabMoney ya maida martani da cewa:

"Duk inda aka ce babu matsalar kuɗi, zaka ga akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba bu wata matsala da zata faru."

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Mace Mai Ciki Da Jaririnta Sun Rasa Rayukansu Saboda Rashin Likitoci a Nasarawa

Wata mai shafin @Her374884 ta ce:

"Abun da daɗin gani amma idan ni ce ba zan yi haka ba."

@nanayaapimaa ta ce:

"Kuɗi na kawo farin ciki."

Karshen Kyau: Budurwa Ta Girgiza Intanet da Bidiyon Santala-Santalan Kawayenta

A wani labarin na daban kuma Wani bidiyo da wata budurwa ta wallafa wanda ya nuna kyawawan ƙawayenta a cikin kayan makaranta ya ja hankali a soshiyal midiya.

Bidiyon ya nuna cauɗa-cauɗan matan waɗanda suka sanya Hijabai farare iri ɗaya da kayan makarantarsu, suna masu yin murmushi yayin da kamara ke ɗaukarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262