Kotu Ta Bada Belin Abba Kyari Bayan Shafe Wata 18 A Gidan Gyaran Hali
FCT Abuja - Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda, DCP, Abba Kyari.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Mai shari'a Kolawole Omotosho ne ya bada balin dan sandan a ranar Alhamis bayan ya shafe wata 18 tsare a gidan gyaran hali, rahoton The Punch.
Hukumar Yaki da Masu Fatauci da Shan Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta ayyana neman Kyari ruwa a jallo kan zarginsa da hannu a badakalar hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hujjar bada belin Abba Kyari
Mai shari'a Omotosho ya ce duba da cewa Kyari da tawagarsa sun ki tserewa a lokacin da aka kai hari gidan yarin Kuje, inda kimanin kashi 90 na fursunoni suka tsere ya nuna cewa Kyari a shirye yake ya fuskanci zargin da ake masa.
Alkalin ya kara da cewa zargin da ake yi wa Kyari ba su kai girman a hana shi beli ba kuma ba a fargabar zai shiga jirgin sama ya tsere daga kasar, Channels TV ta rahoto.
Daga bisani an kama shi a watan Fabrairun 2022 bayan NDLEA ta yi zargin cewa ya taba wasu kwayoyi da aka kwato a matsayin hujja daga wadanda ake zargi da laifi kuma aka tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje.
Amma, har yanzu akwai shari'ar da ake yi da Kyari a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng