Hajjin Bana: An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Alhazan Najeriya Da Dama Suka Kamu Da Rashin Lafiya a Saudiyya

Hajjin Bana: An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Alhazan Najeriya Da Dama Suka Kamu Da Rashin Lafiya a Saudiyya

  • An bayyana cewa alhazan Najeriya da dama sun kamu da rashin lafiya a yayin gudanar da aikin hajjin bana
  • Fiye da rabin alhazan Najeriya dubu 90 da suka sauke farali a bana ne aka tabbatar da sun yi fama da rashin lafiya
  • An alaƙanta hakan da cunkoso da kuma yanayi na matsanancin zafi da aka samu wajen aikin hajjin a bana

An bayyana dalilin da ya sa yawancin alhazan Najeriya suka kamu da rashin lafiya yayin aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Mamba a kwamitin Alhazai na jihar Ogun, Tunde Oladunjoye ne ya bayyanawa jaridar The Punch hakan.

An bayyana abinda ya janyowa mahajjata rashin lafiya
Cunkoso da tsananin zafin yanayi ne suka janyo rashin lafiyar mahajjata da dama. Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Tsananin zafi da cunkoso ne ya janyo rashin lafiya da mutuwar mahajjata

Tunde ya alaƙanta yawaitar rashin lafiyar da aka riƙa samu da abubuwa da dama da suka faru bayan ɗage dokar Covid-19 da ƙasar Saudiyya ta yi.

Kara karanta wannan

Hajjin 2023: Maniyyaciya Daga Kano Ta Rasu A Saudiyya, Abba Gida Gida Ya Yi Martani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce daga cikin abubuwan akwai yanayi na tsananin zafi da aka samu a bana, da kuma cunkoson jama'a a yayin aikin hajjin.

Ya ƙara da cewa hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa aikin hajjin wannan shekarar ya tara mutanen da ba a taɓa tara irinsu a baya ba.

Mahajjatan Najeriya 14 sun mutu yayin aikin hajji

Shugaban tawagar likitocin Najeriya a aikin hajjin bana, Dakta Usman Galadima, ya ce mahajjata aƙalla 14 ne suka rasa rayukansu a yayin aikin hajjin na bana.

Ya Bayyana cewa mahajjatan da suka rasu sun fito ne daga jihohin Kaduna, Filato, Abuja, Borno, Osun, Benue, Yobe da kuma Legas.

Galadima ya ce wasu daga cikin alhazan nan Najeriya sun rasu ne gabanin Arafat, a yayin da wasu kuma daga cikinsu suka rasu ana tsakiyar hawan Arafat.

Kara karanta wannan

Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 Da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta haɗa, ya nuna cewa kusan rabin alhazan Najeriya sama da dubu 90 da suka sauke farali a bana, sun kamu da rashin lafiya.

Daya daga cikin alhazan Kano ta riga mu gidan gaskiya

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata daga cikin mahajjatan jihar Kano, mai suna Hadiza Ismail.

An bayyana cewa ta rasu ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a birnin Makkah na kasar Saudiyya, bayan fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng