“An Sa Ni Yin Haka Ne”: Matashiya Ta Mari Kan Kan Wani Mutum a Motar Kasuwa, Ya Yi Martani a Bidiyo
- Wata matashiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa wani bidiyonta tana marin kan wani mutum da bata sani ba
- A bidiyon wanda ta saki a TikTok, ta yi ikirarin cewa kawarta ce ta ce idan ta isa ta aikata hakan
- Abun bakin ciki, sam matashin bai ji dadin haka ba inda cikin fushi ya lalata wayar budurwar a cikin motar kasuwan
Wata matashiya mai suna @favour_tkb a TikTok ta saki bidiyon matakin da wani mutum da bata sani ba ya dauka bayan ta mare shi a kai.
Ta shiga motar kasuwa tare da kawarta, wacce ta ce idan ta isa ta mari kan mutumin da bata sani ba.
Yarinyar wacce ta cika son wasa sai ta yanke shawarar gwasa abun da aka sa ta amma bayan ta aikata, sai mutumin ya juyo sannan ya tambayeta dalilin da yasa ta mare shi.
“Na Zata Dala Ne”: Magidanci Ya Likawa Matarsa Bandir-Bandir Na Yan N20, Matar Ta Kama Kafafuwansa a Bidiyo
Da ya lura da kamaran, sai ya fusata sannan ya buge wayar daga hannunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da take wallafa bidiyon, matashiyar ta rubuta:
"Kawata tace idan na isa na mari kan wannan mutumin da ban san koye ba. Yanzu kalla yayin da ya bata mani waya. Saura kadan ya yi mun duka fa."
Mutane sun yi martani
@Michaelmicmala ya ce:
"Idan da US ne sai jikinki ya fada maki da kudaden da za ki biya."
@Billzray ya yi martani:
"Duk baku da hankali a kasar nan. Kalli yadda kan wannan ke kara por."
@kellviiiiin ya yi martani:
"Wai menene haka wai."
@Ayomi ya yi martani:
"Na rantse da ni ne sai mutane sun taru a kanmu."
@BIG ADEOLAMI ya ce:
"Baaba na yi dariya har na gaji."
@oluwadamilola ya yi martani:
"Allah ne zai saka mai. Omoh ni da mashin ya jefar yanzu na ga wannan ina dariya."
@Shawty ta yi martani:
"Ke da kawarki duk baku da hankali."
@zee ta yi martani:
"Wannan bai dace ba. Da ya naushe ki a fuskanki fa."
Matashi ya yi wa matarsa ruwan kudi yan N20 don nuna farin ciki
A wani labari, wani bidiyo da ya yadu a dandalin TikTok ya nuno wani magidanci yana yi wa matarsa yayyafin kudi bandir-bandir na yan N20 yayin da ita kuma ta durkusa a gabansa.
Mutumin ya nuna kamar yana nuna godiyarsa ga matar tasa ce wacce ke goye da kyakkyawan yaro a bayanta inda shi kuma ya ci gaba da yi mata yayyafin kudi.
Asali: Legit.ng