Dan Najeriya Ya Koka, Ya Turowa 'Yan Uwansa Kudade Su Gina Masa Gida Amma Suka Cinye
- Wani ɗan Najeriya da ke zaune a ƙasar waje, ya gano cewa 'yan uwansa sun wawashe kudaden da ya aika musu domin gina masa gida
- Mutumin wanda ke zaune a Amurka ya gano hakan ne bayan shekaru shida yana aiko da kuɗi don a gina masa gida
- Ya gano cewa ‘yan uwansa sun shirga masa karya ne kawai, babu wani gida da suka gina masa, kuma sun kashe kuɗaɗen da ya turo
Wani ɗan Najeriya ya riƙa aikowa da 'yan uwansa kuɗaɗe daga Amurka da zummar su gina masa gida.
Amma shekaru shida a cikin hakan, ya gano cewa basu gina masa gidan ba, kuma sun kashe duk kuɗaɗen da ya turo musu.
'Yan uwan mutumin sun masa ƙaryar cewa aiki na tafiya
Wani mai suna Mazi Echidime da ya wallafa labarin a shafinsa na Tuwita, ya ce 'yan uwan mutumin sun masa ƙaryar cewa aiki yana tafiya domin su ci gaba da tatsar kuɗaɗe daga wajensa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Echidime ya ce an kira kamfaninsa domin ya je ya duba ko a wane mataki ne aka tsaya a ginin gidan.
Ya wallafa hotunan gidan a shafin nasa na Tuwita, wanda ke nuni da matakin da ake a aikin gidan.
Martanin da masu amfani da Tuwita suka yi dangane da kuɗaɗen ginin gida da aka cinye
@OGBENI_BAMBAM ya ce:
“Na gaji da jin irin wannan labarin”
@derealeMorgan ya ce:
“Nagodewa ɗan uwana, domin kuwa nawa yana tafiya cikin sauri, saboda ƙididdigewar da yake da kuma riƙon amanarsa.”
@shizzlecrown ya ce:
“Ka bi a hankali Mazi, kafin su riƙa kallonka matsayin maƙiyinsu.”
@quincypetersjr ya ce:
“Wai dama har yanzu mutane suna aiko da kuɗi don a yi musu gini? Na zata kowa ya fahimci yadda abubuwa ke wakana”
Wani matashi ya samu maƙudan kuɗaɗe da gadar katako da ya haɗawa masu babura
Legit.ng a baya ta kawo muku labarin wani matashi da ya haɗa gadar katako domin masu babura su riƙa wucewa ta kai.
A wani ɗan guntun bidiyo da ya karaɗe Intanet, an hangi masu babura na yin layi don tsallake ƙaramar gadar katakon da aka yi a kan hanyar ruwa.
Asali: Legit.ng